Majalisar Dattawan Amurka ta amince da dokar nan da za ta bai wa gwamnatin Joe Biden damar ware wa kasar Ukraine tallafin Dala biliyan 12.3 don karfafa mata ci gaba da yaki da Rasha.
Dokar ta samu amincewar majalisar ne bayan kuri’ar jin ra’ayi da sanatocin suka kada a ranar Alhamis, inda mutum 72 suka amince, 25 suka ce a’a.
- Harin Rasha ya hallaka fararen hula 23 a Ukraine
- Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami awa 5 bayan Kamala Harris ta bar yankin
Ana sa ran ita ma Majalisar Wakilan Amurka za ta bi sahu wajen amincewa da dokar kafin daga bisani a gabatar wa Shugaba Biden ya rattaba mata hannu.
Kazalika, dokar ta amince a debi Dala biliyan $3.7 daga kudin makaman Amurka a mika wa Ukraine.
Ko a farkon wannan shekarar, Amurka ta bai wa Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy tallafin kudi na Dala biliyan 13.6 domin kara masa karfi a yakin da suke gwabzawa da Rasha.
Haka nan, Amurka ta sake tura wa Ukraine makudan kudi Dala biliyan $40 a matsayin tallafi sakamakon yakin da kasar ke yi da Rasha.