✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisar Dattijai ta ki amincewa Kaduna ta ciwo bashin kudi

Majalisar Dattijai ta ki amince wa Jihar Kaduna ta ciwo bashin kudi $350m bayan kusan shekara daya da jihar ta neman hakan. Kin amincewar ya…

Majalisar Dattijai ta ki amince wa Jihar Kaduna ta ciwo bashin kudi $350m bayan kusan shekara daya da jihar ta neman hakan.

Kin amincewar ya biyo bayan amincewa da rahoton da kwamitin sanata Shehu Sani ya gabatar a gaban majalisar.

A cewar Shehu Sani, idan aka ciwo bashin, kudin da ake bin Kaduna zai zama Dala miliyan 532 daga Dala miliyan 232. Sannan kuma ya ce yanzu haka jihar ce ta biyu wajen yawan bashi.

Shi ma sanata Suleman Othman Hunkuyi, ya ce bashin kudin ba shi ne abin da jihar ke bukata, sannan shi ma sanata Danjuma La’ah ya ce lallai kada a amince da ciwo bashin.