Majalisar Dinkin Duniya na bukatar a gaggauta sako daliban makarantar Kankara | Aminiya

Majalisar Dinkin Duniya na bukatar a gaggauta sako daliban makarantar Kankara

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres
    Sani Ibrahim Paki

Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah-wadai da harin da ake zargin ‘yan bindiga sun kai wa daliban makarantar sakandiren gwamnati ta GSSS Kankara a jihar Katsina.

Martanin Magatakardar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin majalisar, Stephane Dujarric ya fitar a birnin New York ranar Litinin.

Ya kuma yi kira da a gaggauta sakko daliban kusan 300 da ake zargin an sace su ba tare da wani sharadi ba.

Sanarwar ta ce, “Babban Magatakardar yana matukar Allah-wadai da harin da aka kai makarantar sakandiren dake jihar Katsina a Najeriya ranar 11 ga watan Disamba.

“Yana kuma jaddada cewa hari a kan makarantu da sauran cibiyoyin ilimi babban laifi ne da ya ke yi wa hakkin dan Adam karan tsaye,” inji shi.

Daga nan sai Mista Guterras ya yi kira ga hukumomin tsaron Najeriya kan su gaggauta gano yaran tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a ciki gaban kuliya.

Ya kuma ce Majalisar za ta ci gaba da tallafa wa Gwamnatin Najeriya ta kowacce fuska a kokarin da take yi na yaki da ‘yan ta’dda da kuma munanan akidu.

A makon da ya gabata ne dai wasu mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne suka mamaye makarantar tare da sace dalibai maza da dama wadanda ya zuwa yanzu ba a kai ga tantance adadinsu ba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fara hutun mako daya a garinsa na Daura dake jihar ta Katsina.