Majalisar Dinkin Duniya ta roki Amurka ta rufe kurkukun Guantanamo | Aminiya

Majalisar Dinkin Duniya ta roki Amurka ta rufe kurkukun Guantanamo

Gidan kurkukun Guantanamo
Gidan kurkukun Guantanamo
    Muhammad Aminu Ahmad

Wadansu kwararru na Majalisar
Dinkin Duniya sun bukaci Amurka ta gaggauta rufe kurukukun Guantanamo da ta kafa kimanin shekara 20 da suka gabata don daure wadanda take zargi da aikata ayyukan ta’addanci.

Masu binciken, wadanda Majalisar Dinkin Duniya ta nada domin yin nazari game da zarge-zargen cin zarafin dan Adam da Amurka ke yi a gidan yarin, sun bayyana kurukukun wanda Amurka ta bude bayan harin 11 ga Satumban 2001, a matsayin cibiyar azabtarwa da cin zarafin mutane ba tare da an tabbatar da sun aikata wani laifi ba.

Kwararrun sun bukaci Gwamnatin Amurka ta mayar da mutanen da aka tsaren kasashensu na asali ko wasu wurare na daban, sannan ta samar musu da maganin warkar da azabar da suka
dandana.

Kwararrun sun ce, gidan yarin na Guantanamo yana kunshe da bala’i, inda ake amfani da shi wajen keta hakkin dan Adam.

Har yanzu akwai mutum 39 daga cikin 700 da aka tsare a gidan yarin na Guantanamo, amma kawo yanzu tara kadai ne aka tuhuma kan aikata
miyagun laifuffuka.

A can baya, an ba da rahoton cewa, akwai fursunonin da suka kashe kansu a gidan yarin saboda irin masifar da suka
dansana kuma babu wanda aka tuhuma daga cikinsu da aikata laifi a cewar kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya.