Majalisar dokokin Bauchi ta amince da dokar kafa jami’ann tsaro mallakin jihar | Aminiya

Majalisar dokokin Bauchi ta amince da dokar kafa jami’ann tsaro mallakin jihar

    Abubakar Muhammad Usman

Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta amince da wata doka da za ta bayar da damar samar da jami’an tsaro mallakar jihar don magance kalubalen tsaro.

Gwamnan Jihar, Bala Mohammed, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan wani dattijo mai suna Jauro Dakkuna mai shekara 75.

’Yan bindiga ne dai suka kashe mutumin a yankin Shafa da ke Karamar Hukumar Alkaleri ta jihar.

Mohammed, ya ce gwamnatin jihar na shirin daukar matasa sama da 2,000 aikin tsaro a jihar.

Gwamnan ya kara da cewa ’yan bindigar da suka addabi yankin suna da masu taimaka musu

Ya ce: “Ba yadda za a yi wani ya taso daga Zamfara ya zo wannan kebabben waje a Shafa don ya kashe wani sai dai idan yana da mai taimaka masa.

“Kamar yadda hukumomin tsaro suka saba fada, irin wannan abu ba zai iya faruwa ba sai an hada kai da wasu a cikinmu.

“Dole ne mu ji tsoron Allah a dukkan al’amuranmu, mun bukaci Hakimai biyu na yankin da su tabbatar sun zama masu bin doka da oda, su zama masu sanya ido don nemo bayanai game da ’yan bindigar.

“Rahotannin da suka zo min a jiya akwai wasu mutanen yankin da ke kai wa ’yan bindiga kayan abinci a daji, don haka muna sane da irin wannan koma-baya, akwai wasu ’yan tsirarun jami’an tsaro da ke yin sulhu da ’yan bindigar.

“Don haka, muna rokon Kwamishinan ’Yan Sanda da sauran jami’an tsaro da su sauya ko turo karin jami’an tsaron da za su yaki ’yan bindiga,” inji Gwamnan.

Mohammed ya kara da tabbatar wa mazauna garin cewa za a samar da hanyar da za a bi don inganta yanayin tsaro.

“Mun kafa tsarin amsa tambayoyi, kuma na samu labarin wasu na kai wa ’yan bindigar a wuraren da suke a boye hatsi da fulawa, wannan shi ne rahoton da na samu, kuma za mu dauki mataki kan hakan.

“Za mu dauki mataki a kan ire-iren wadannan mutane a duk inda suke,” a cewar Gwamnan.

Bala Mohammed ya kuma shawarci jama’a da su bai wa gwamnatin jihar bayanai ta hannun shugabannin kananan hukumominsu kamar Ciyamomi da Kansiloli da masu unguwanni domin daukar matakin gaggawa don dakile duk wata barazanar tsaro.