Majalisar Dokokin Kano ta zabi sabon Shugaba | Aminiya

Majalisar Dokokin Kano ta zabi sabon Shugaba

Majalisar Dokokin Jihar Kano
Majalisar Dokokin Jihar Kano
    Muhammad Bashir Amin

Mambobin Majalisar Dokokin jihar Kano sun zabi mamba mai wakiltar mazabar Makoda a zauren Majalisar, Hamisu Chidari a matsayin sabon Shugaba.

Zaben nasa ya biyo bayan ajiye mukamin da tsohon Shugaba, Abdulaziz Gafasa, da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Kabiru Dashi suka yi da a tsakar dare ranar Litinin.

Gafasa ya bayyana saukar tasa a wata wasika da ya aike wa zauren majalisar mai dauke da kwanan Satan 14, ga Satan Disamban 2020.

Wasikar ta bayyana cewa: “Ni Rt. Hon. Abdulaziz Garba Gafasa na rubuta wannan takarda don shaidawa masu girma ’yan majalisa da dukkan jama’a, cewa na sauka daga mukamina na shugabancin zauren Majalisar Dokokin Jihar Kano daga ranar 14, ga watan Sisamba, 2020, bisa dalilai na kashin kai.

“A karshe ina gode wa mambobin Majalisa bisa hadin kai da goyon bayan da suja ba ni lokacin da nake jagorantar zauren majalisar, sannan ina addu’ar Allah Subhanahu Wata’ala Ya yi wa sabon shugabancin majalisar jagoranci”.

Ranar Talata, wani ma’aikaci a zauren Majalisar wanda ya bukaci a boye sunansa saboda ba a ba shi damar magana da ’yan jarida ba, ya tabbatar da ajiye mukamin na Gafasa tare da Shugaban Masu Rinjayen.

Ragowar mutanen biyun da suka ajiye mukamansu kamar yadda majiyar ta sanar mana, su ne Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar, Kabiru Dashi da mataimakinsa, Tasi’u Zabainawa.

Duk da cewa ba su bayyana dalilan ajiye mukamansu nasu ba, amma dalilan ba za su rasa nasaba da zaben fitar da ’yan takara da jam’iyyar APC mai mulki a jihar da ta gudanar a kwanakin baya ba da kuma yunkurin da ake yi na tsige su.