✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dokokin Pakistan ta zabi jagoran ’yan adawa sabon Firaminista

Tsohon Firaminista Imran Khan ya ce akwai hadin bakin Amurka a yunkurin tsige shi.

Majalisar Dokokin Pakistan ta zabi Mohammad Shahbaz Sharif jagoran ’yan adawa a matsayin sabon firaminista wanda ya maye gurbin Imran Khan da majalisar ta tsige a karshen mako.

Sabon Firaminista Mohammad Shahbaz Sharif yana da jan aiki farfado da tattalin arzikin kasar da samar da ci-gaban da ake bukata.

Shi dai Shehbaz Sharif ya kasance dan uwa ga tsohon Firamini Nawaz Sharif wanda sau uku yana rike mukamin na firaminista.

Sharif ya lashe zaben zama firaministan kasar ta Pakistan da kuri’un ’yan majalisar dokoki 174 daga cikin ’yan majalisa 342.

A Lahadin da ta gabata ce Majalisar Dokokin Pakistan ta kada kuri’ar yanke kauna da gwamnatin tsohon firaminista Imran Khan bayan shafe makonni ana rikicin siyasa a kasar.

Babu wani Firaministan da ya taba yin cikakken wa’adi a Pakistan, amma Khan shi ne na farko da ya rasa mukaminsa ta hanyar kada kuri’ar rashin gamsuwa da gwamnatinsa.

Imran Khan ya dage kan cewa akwai hadin bakin Amurka a yunkurin tsige shi, sai dai Amurkan ta musanta hakan.