✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dokokin Tarayya ta yi wa Dokar Zabe kwaskwarima

A yanzu an amince kowace jam’iyya ta zabi gwanaye a bisa tsarin da suke so.

Majalisar Dokokin Tarayya ta yi wa Dokar Zabe kwaskwarima, inda a yanzu an amince kowace jam’iyyar siyasa ta gudanar da zaben fidda gwanayen takara ta kowane irin salo ta yi ra’ayi.

Wannan dai ya biyo bayan sake gabatar da kudirin da Sanata Yahaya Abdullahi daga Majalisar Dattawa da kuma Honarabul Abubakar Hassan Fulata daga Majalisar Wakilai ta Tarayya suka yi yayin zaman majalisun biyu a ranar Laraba.

Majalisar ta fara yin gyaran gaggawa kan kudiri na 87, wanda ya yi magana kan irin zaben fidda-gwanin ’yan takara daga kowace jam’iyyar siyasa.

A yanzu an amince kowace jam’iyya ta zabi gwanayen a bisa tsarin ’yar tinke, kato-bayan-kato ko zaben game-gari.

Da farko dai Kudirin Gyaran Dokar Zabe ya amince a yi zaben kai-tsaye, ba na wakilan jam’iyya ba, wato yin amfani da ‘delegates’ wajen fidda dan takara.

Wannan shi ne tsarin da ake kai a kasar nan, wanda kuma kokarin kawar da shi a zaben 2023 bai yi nasara ba, biyo bayan fatali da tsarin zaben kai-tsaye da Buhari ya yi bisa dalilin cewa zai lakume kudade wajen gudanarwa.

An amince da Kudiri na 84, wanda ya bada damar ko jam’iyya ta yi zaben kai-tsaye ko kuma tsarin wakilan jam’iyya, wato ‘delegets’.

An kuma amince da Kudiri na 84(2), wanda ya bad a damar cewa jam’iyya za shirya zaben fidda gwani ta hanyar wakilai, ko kumà a cimma yarjejeniyar tsayar da wani ba tare da an yi zabe ba.

A kwaskwarimar da aka yi wa kudirin dokar, zaben fidda-gwamnin dan takarar shugaban kasa, an gindaya cewa tilas sai an yi Babba Taron Jam’iyya a kowace jiha 36 da Abuja, domin wakilan jam’iyya daga mazabu su yi zaben ’yan takara.

Haka nan kuma kudirin ya ce za a shirya babban zabe na kasa, inda za a jaddada dan takarar da ya fi sauran ’yan takara yawan kuri’u.

A jiya Talata ne aka ruwaito Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawal yana ce “za mu yi wa Kudirin Gyaran Dokar Zabe Kwaskwarima, mu sake aika wa Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu.’

Bayanai sun ce Sanata Lawan ya bayyana cewa Majalisun Tarayyar biyu za suyi zaman yi wa Kudirin Gyaran Dokar Zabe Kwaskwarima a ranar Laraba, domin a cire wuraren da ake tababa, sannan su sake aika wa Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu.

Lawan ya fadi hakan ne a ranar Talata da dare, yayin da ya ke ganawa da manema labarai, bayan ganawar da ya yi a kebance tare da shugaban kasar.