✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Kano ta ba Ganduje awa 48 ya kori shugaban hukumar haraji

Daga matsayi na biyu, Jihar Kano ta koma ta 10 wajen yawan kudaden shiga.

Majalisar Dokokin Kano ta bukaci Gwamnan Jihar, Abudullahi Ganduje ya sallami Shugaban Hukumar Kabar Haraji ta jihar  (KIRS) AbduRazak Salihi, cikin sa’a 48. 

Majalisar ta shawarci Gwamna Ganduje ya sallami AbduRazak Salihi, ne saboda samun sa da laifin saba kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma yi wa majalisa tsaurin ido.

Zaman Majalisar na ranar Talata ya dauki matakin bayan Shugaban na KIRS ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi kan aikace-akacen hukumar a karkashinsa.

Shugaban Majalisar, Injiniya Hamisu Chidari, ya ce daukar matakin ya zama dole saboda da karairayin da kuma halayyar da shugaban hukumar ya nuna a lokacin da yake amsa tambayoyi.

Ya ce Shugaban na KIRS ya ki bayyana wa Majalisar kudaden da hukumar ta tara, duk da cewa Majalisar ta sha neman hakan daga gare shi; Amma ya rubuta rahoto a kan kudaden harajin, ya aike wa gwamnatin jihar ta hannun Babban Sakataren Hukumar kula da Filaye.

Majalisar ta zargi shugaban na KIRS da hada baki da gwamnatin jihar inda suka yi gaban kwansu suka rage farashin harajin da ake karba daga Kungiyar Dillalan Man Fetur (IPMAN) daga N250 zuwa N100, wanda hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

’Yan majalisar sun bayyana fushinsu kan abin da suka kira gazawar Shugaban na KIRS da kuma rashin sanin makamar aikinsa kan harkar tara kudaden shiga.

Shugaban Majisar ya ce sun kafa kwamitin mutum takwas domin gano dalilin da Jihar Kano ta sauka daga matsayi na biyu zuwa na 10 a jerin jihohin mafiya yawan tara kudaden shiga a Najeriya.

Kwamitin, karkashin jagorancin Shugaban Kwamitin Kudade na Majalisar, Magaji Dahiru Zarewa, zai kuma binciki abubuwan da shugaban hukumar ya aikata; sannan ya mika rahotonsa cikin wata daya.

A lokacin zama Majalisar dai an ga jikin shugaban yana karkarwa, ya kasa amsa tambayoyi aka yi masa kan yin gaban kansa da ya yi na rage farashin haraji da kuma yi wa Majalisar danwaken zagaye.