✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rundunar ‘yan sandan Kano ta gayyaci Muhuyi Magaji

A halin yanzu Muhuyi Magaji yana hannu jami'an 'yan sanda.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta gayyaci Muhuyi Magaji Rimin Gado, Shugaban Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci ta Kano (PCACC) da aka dakatar.

Wannan na zuwa ne bayan shawarar da Majalisar Dokokin Jihar ta bayar na cafke shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

  1. Karin dalibai 3 sun kubuta daga hannun ’yan bindiga a Kaduna
  2. Buhari ya sanya hannu kan karamin kasafin N982bn

Kwamitin da aka kafa domin binciken Barista Muhuyi ya gabatar da kudirin bukatar hakan ne yayin zaman Majalisar na ranar Litinin wanda shugabanta, Hamisu Ibrahim Chidari ya jagoranta.

A yayin zaman da Majalisar ta yi a kan kudirin, ta tattauna kan shawarwarin kwamitin mambobi 12 da aka kafa domin binciken Rimin Gado.

Shugaban Kwamitin, Alhaji Umar Musa Gama ya bayyana cewa sun kammala bincikensu kuma kwamitin ya yi tanadin wasu shawarwari biyar.

A cewarsa, daya daga cikin shawarwarin sun hada da korar shugaban da aka dakatar nan take.

Haka kuma, akwai bukatar a kama shi tare da gurfanar da shi sannan a kafa kwamitin wucin-gadi da zai binciki duk wata harkalla ta kudi da aka gudanar a PCACC daga 2015 zuwa yanzu.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaman, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Alhaji Labaran Abdul Madari, ya ce kwamitin hadin guiwar da aka kafa don binciken Rimin Gado ya gano takardar bogi da lauyansa ya gabatar.

Kazalika, kwamitin ya ba da shawarar cewa Hukumar Ma’aikatan Gwamnati ta Jihar da ta dauki matakin da ya dace kan Isah Yusuf, jami’i na hudu da ke matsayin akanta a PCACC.

Madari, ya ce kwamitin ya kuma yi kira ga akantan da Rimin Gado ya ki amincewa da shi ya fara aiki nan take.

Aminiya ta ruwaito cewa, zaman Majalisar ya dauki tsawon minti 30 ne kawai, inda ta karbi rahoton sannan ta dage zamanta zuwa ranar Talata.

Tun a farkon watan Yulin nan ne Majalisar ta dakatar da Muhuyi da ke zaman Shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin hanci da Rashawa (PCACC).

Majalisar ta dakatar da shi ne saboda kin karbar sabon akantan da Akanta-Janar na Jihar Kano ya tura wa Hukumar.

Dakatarwar, wacce ta fara aiki nan take, ta biyo bayan samun takardar  korafi da Majalisar ta yi daga Ofishin Akanta-Janar din ne a kan lamarin.