✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Legas ta amince da dokar haramta yawon kiwo

Ta kuma amince da sabuwar dokar karbar harjin VAT a Jihar.

Majalisar Dokokin Jihar Legas ta amince da dokar haramta yawon kiwo a fadin jihar.

Zaman majalisar na ranar Alhamis ya kuma amince da dokar karbar harajin VAT kan kayayyakin da mutane ke saye.

Bayan amincewar zauren Majalisar, Shugaban Majalisar, Mudashiru Obasa, ya umarci Mukaddashin Akawun Majalisar, Olalekan Onafeko, ya mika kwafin kudurorin dokar ga Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.