✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Mali ta amince sojoji su mulki kasar na tsawon shekara biyar

Hakan ya yi daidai da bukatar da sojojin suka gabatar.

Majalisar Dokokin Mali ta amince da wani kudirin doka da zai bai wa sojoji damar jagorantar kasar har tsawon shekaru biyar masu zuwa, duk da takunkuman da aka kakaba wa kasar sakamakon jinkirta gudanar da zabe.

Tun bayan da suka karbe mulki a cikin watan Agustan 2020, sojojin Mali suka yi alkawarin gudanar da zabe a cikin watan Fabrairun wannan shekara a kasar da ke yankin Sahel.

Sai dai a cikin watan Disamban da ya gabata, sojojin suka bukaci ci gaba da kankamewa kan karaga tsakanin watanni shida zuwa shekara biyar, suna masu kafa hujja da matsalar tsaro.

Tuni Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS ta lafta jerin takunkumai kan Mali a matsayin martini, inda ta kuma rufe kan iyakokin kasar.

ECOWAS ta kuma yi watsi da matakin sojojin na tsawaita zamansu kan karagar mulkin kasar.

A wannan Litinin ne, mambobin rikon kwarya a majalisar dokokin Malin 120 daga cikin 121 suka kada kuri’ar amince wa sojojin ci gaba da mulki har zuwa shekaru biyar nan gaba, abin da ya yi daidai da bukatar da sojojin suka gabatar tun a can baya.

Sannan babu wani bayani game da takamammiyar ranar da za a gudanar da zabe koda shekaru biyar din sun cika kamar yadda Gidan Rediyon Faransa na RFI ya ruwaito.