✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisar Pakistan ta sauke Firaminista Imran Khan

Khan shi ne na farko da ya rasa mukaminsa ta hanyar kada kuri’ar rashin gamsuwa da gwamnatinsa.

Majalisar Dokokin Pakistan, ta kada kuri’ar sauke Firaministan kasar Imran Khan a Lahadin nan.

An dai sauke Imran Khan ne bayan shafe makonni ana rikicin siyasa a kasar ta Pakistan.

Mukaddashin kakakin majalisar kasar Sardar Ayaz Sadiq ya ce ’yan majalisa 174 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudirin yankan kauna kan jagorancin tsohon Firaminista Imran Khan.

Babu wani Firaministan da ya taba yin cikakken wa’adi a Pakistan, amma Khan shi ne na farko da ya rasa mukaminsa ta hanyar kada kuri’ar rashin gamsuwa da gwamnatinsa.

Ba a dai fayyace lokacin da majalisar Pakistan din za ta zabi sabon Firaministan kasar ba.

Tun a ranar Asabar da ta gabata ce Kotun Kolin kasar ta yanke hukuncin dole a kada kuri’ar yanke kauna da gwamnatinsa.

Majiyoyi daga Islamabad sun ruwaito cewa tun gabanin wannan mataki Khan ya ki yarda a yi kuri’ar domin ya san ba zai kai labari ba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da masu adawa da shi suka shirya tsaf domin hambarar da shi da kuma tsayar da nasu dan takarar.

Imran Khan ya dage kan cewa akwai hadin bakin Amurka a yunkurin tsige shi, sai dai Amurkan ta musanta hakan.