✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Sakkwato ta amince da dokar nakasassu

Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta amince da dokar hana nuna wariya ga nakasassu a jihar. Hakan na zuwa ne bayan bukatar da Hon. Maidawa Kajiji…

Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta amince da dokar hana nuna wariya ga nakasassu a jihar.

Hakan na zuwa ne bayan bukatar da Hon. Maidawa Kajiji (APC-Shagari) da Hon. Abubakar Magaji (PDP- Bodinga ta Arewa), suka gabatar a zaman Majalisar ta ranar Laraba.

Kudirin ya samu karatu na farko da na biyu ne a ranar 23 ga Yulin 2020 kafin a mika shi ga Kwamitin Kula da Walwala da Bunkasa Al’adu da Kyautata Rayuwa na Majalisar.

Da yake gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin, Hon. Kabiru Dauda, ya ce kwamitin ya gana da duk masu ruwa da tsaki kan batun.

“A lokacin taronmu kwamitin ya lura cewa wasu bangarorin kudirin ba su da mahimmanci.

A cewarsa, wasu bangarorin ba su dace da tsarin zamani na tsara dokoki ba kuma duk an gyara kura-kuran rubutu.

Daga baya ‘yan majalisar sun amince da rahoton kwamitin sannan suka aminci da kudirin.