✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Tarayya ta karyata rahoton samamen DSS

Ta ce bidiyon labarin karya ne

Majalisar Tarayya ta karyata rahoton da ke cewa jama’ian hukumar DSS sun mamaye harabarta a ranar Laraba.

Ta bayyana hakan ne cikin sanarwa a safiyar Alhamis ta bankin Daraktan Yada Labaranta, Agada Rawlings Emmanuel , inda ta ce bidiyon da aka yada kan batun ba gaskiya ba ne.

“Hankalin hukumar gudanarwa ta Malalisar Tarayya ya kai kan wani bidiyon da aka yada a Twitter na wani @Chukwuebuka, wanda ya yi zargin jami’an DSS sun mamaye harabar Majalisar Tarayya.

“Bidiyon wanda ba a tantace ba na wani batu ne da ya auku a 2018 a babbar kofar shiga Majalisar wanda a yanzu ana gab da kammala aikin gyaranta.

“Don haka ba mu san manufar da yake nufin cim ma wa ba da sake yada bidiyon duba da yanayin siyasar kasa da karatowar zabe,” in ji sanarwar.

Emmanuel ya ce hukumar Majalisar na kira ga ’yan Majalisar da ma’aikatanta da ma ’yan kasa baki daya da su yi watsi da bidiyon saboda labarin karya ne.

Ya kara da cewa, ’yan majalisa na hutu a halin yanzu, kuma babu wata mamaya da sauran ma’aikata suka fuskanta daga jami’an na DSS.

Ya ce sabon Akawun majalisar, Sani magaji Tambuwal tare da sauran ma’aikata na aiki tukuru wajen tafiyar da harkokin Majlisar yadda ya kamata