✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Tarayya ta ki yarda a dandake masu fyade

Majalisar Wakilai ta yi watsi da kiran da aka yi na zartar wa wadanda aka samu da laifin fyade hukuncin dandaka. Majalisar ta dauki matakin…

Majalisar Wakilai ta yi watsi da kiran da aka yi na zartar wa wadanda aka samu da laifin fyade hukuncin dandaka.

Majalisar ta dauki matakin ne ranar Alhamis bayan kiraye-kirayen da aka yi sakamakon yawaitar rahotannin fyade da ake samu a Najeriya.

Hakan ne ya sa dan majalisa James Faleke ya bukaci a yi dokar dandaka ko fidiye masu aikiata fyade a kasar.

Da yake mayar da martani a kan kudirin, Shugaban Majalisar Femi Gbajabiamila ya tambayi Faleke cewa. “Su kuma matan da suka yi wa mazan da suka fi karfi fyade wane hukunci za a yi musu?”

Wannan batu ya janyo ka-ce-na-ce a majalisar.