✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Zartarwa ta amince a tsawaita shekarun ritayar malamai

Shugaban Kasa Buhari ya amince da wani tukwici na musamman ga hazikan malamai.

Majalisar Zartarwa ta Tarayya a Najeriya ta amince da wani kudiri na tsawaita shekarun ritayar malamai a fadin kasar.

Kudirin ya nemi a tsawaita shekarun ritayar malaman daga shekara 60 zuwa 65 sannan kuma ya nemi kara wa malamai wa’adin da za su iya dauka suna aiki daga shekara 35 zuwa 40.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai na fadar Shugaban Kasa bayan zaman Majalisar wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Laraba.

Ya ce a yanzu za a mika kudirin zuwa Majalisar Dokokin Tarayyar Kasar domin neman sahalewarta kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya yi tanadi.

Ministan ya ce gwamnati ta yanke shawarar tsawaita shekarun ritayar ne a matsayin wani tukwici ga sadaukarwar malamai a kan aikinsu sannan kuma da manufar kwadaitar da karin ’yan Najeriya wajen fada wa aikin karantarwa.

Ya kara da cewa, Shugaba Buhari ya amince a kan biyan alawus na musamman ga malaman da ke koyar da darussan kimiyya da kuma wadanda ke koyarwa a yankunan karar domin kara musu karsashi.

Ya ce, “Wannan kudiri da Ma’aikatar Ilimi ta amice da shi babban mataki ne kan aniyar da muka kulla tun a shekarar da ta gabata tare da amincewar Shugaban Kasa a kan wani tukwici na musamman ga malamai.”

“Saboda haka, a taron da muka yi a yau, Majalisar Zartarwar ta amince da kudirin wanda aka yi wa lakabi da ‘Kudirin Daidaita Shekarun Ritayar Malamai na 2020’ wanda za a aike wa Majalisar Dokokin Tarayya domin ya samu sahalewarta wajen shigar da shi cikin doka ta yadda duk alkawuran da Shugaban Kasa ya dauka za su samu gindin zama.”

“Makasudin wannan kudiri wanda ke neman amincewar doka shi ne shimfida sabon tsarin tsawaita shekarun ritayar malamai daga shekara 60 zuwa 65 sannan kuma a kara wa’adin aikin malunta daga shekara 35 zuwa 40.”

“Manufar hakan ita ce don janyo hankalin hazikai zuwa ga aikin malunta wanda don haka Shugaban Kasar ya amince a sake bijiro da bayar da kyaututtukan kudi, inganta nagartar malamai da kuma walwala da jin dadinsu.”

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, kafin wannan sabon ci gaba da aka samu, shekarun ritayar malamai a kasar sun tuke ne a kan shekaru 60 yayin da kuma na dadewa a bakin aikin suka tuke a kan shekara 35.