✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisun jihohi da suke amfani da Hausa yayin muhawara

Aminiya ta gano akwai majalisun Arewa da suka amince su yi muhawara da Hausa.

Majisun dokoki na jihohi, majalisu ne suke tattaunawa tare da yin dokokin da za a yi amfani da su wajen tafiyar da harkokin jihohinsu domin jin dadi da walwalar jama’a.

Binciken Aminiya ya gano cewa akwai majalisun wasu jihohin Arewa da suka amince a yi muhawara da Hausa don amfanin mutanen jihohin.

‘An fi magana a Majalisar Jihar Kano da Hausa’

A Jihar Kano, Aminiya ta tattauna da Alhaji Kabiru Hassan Dashi, dan majalisa mai wakiltar Kiru a Majalisar Dokokin Jihar Kano, inda ya ce tun farko dama majalisar ta amince cewa za a yi amfani da harsuna biyu wato Ingilishi da Hausa.

Ya ce, “Mu dama tun farko ba mu amince harshe daya za a yi amfani da shi a majalisa ba. Mun bar shi a bude a tsakaninmu duk harshen da mutum yake son gabatar da kudiri ko wani abu a gaban majalisa zai yi da harshen da ya zaba. Sai dai duk da haka idan kin duba za a ga cewa mun fi yin muhawara da sauran magangannunmu a cikin Harshen Hausa.”

Da yake bayanin dalilin da ya sa suka zabi yin magana da Harshen Hausa a majalisar, wakilin na Kiru ya ce sun yi haka ne domin al’ummar jihar wadanda mafi yawansu ba su jin harshen Ingilishi.

“Tun farko mun amince da yin muhawara da Hausa a majalisa domin amfanin al’ummarmu wadanda yawancinsu ba su jin Ingilishi. Idan mun yi da Huasa mutanen Kano za su fi fahimtar abubuwan da suke gudana a majalisar. Kuma za ki ga ko tattaunawa za mu yi da manema labarai mukan yi da Hausa saboda al’ummarmu wadanda muke wakilta su san irin abubuwan da muke gabatarwa a majalisar,” inji shi.

Da Aminiya ta binciki batun rubuta batutuwan da suka gudana a majalisar, musamman matsayar da aka cimma ko dokokin, sai Alhaji Dashi ya ce ana yin wannan rubutu ne kawai da Harshen Ingilishi saboda wadanda ba Hausawa ba ne za su so karbar kwafin takardun musamman dokoki.

“Kin san da yake abin ya shafi majalisa kuma majalisar akwai takwarorinta a wasu jihohi, to wasu lokuta ’yan majalisar wasu jihohin sukan zo su karbi kwafin dokoki daga hannun wasu majalisun. Kin ga idan ’yan Kudu ne kuma suka zo karbar takardun yaya za a yi su iya fahimta? Haka kuma a wasu lokutan ’yan kungiyoyi masu zaman kansu sukan zo su karbi kwafin takardun dokokin su yi amfani da su, idan da Harshen Hausa aka rubuta, to dole sai an tafi neman masu fasarar da sauransu,” inji shi.

‘A Kudu ma suna amfani da harsunansu’

Da Aminiya take tattauanwa da shi, dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Birni da Kewaye, Alhaji Salisu Ahmed Gwangwazo ya ce, “Akwai doka da ta bayar da dama cewa za a iya amfani da harshen da mambobin majalisa suka amince da shi ko kuma harshen garinsu ko jiharsu.

“Don haka aka amince da yin amfani da Harshen Hausa. Idan kika je jihohin Yarbawa ko Ibo za ki ga su ma suna amfani da harsunansu a majalisunsu.

“Aiki ne da muke yi don al’umma kuma ya dace a fada musu da harshen da suka fi fahimta. Duk da cewa mukan yi amfani da Ingilishi amma mun fi yi da Harshen Hausa.”

A cewarsa, ana rubuta zaman majalisa da Harshen Ingilishii maimakon Hausa ne domin rubutun da ake yi ana ajiye shi ne don mika wa ga gwamnati a matsayin doka ko wani abu makamancin haka wanda kuma a tsarin aikin gwamnati da Harshen Ingilishi ake gudanar da irin wadancan ayyuka.

‘Dokar kasa ta amince a zabi harshen da za a yi amfani da shi’

A Jihar Bauchi, Aminiya ta gano cewa ana amfani da Harshen Hausa a duk lokacin da ’yan Majalisar Dokokin Jihar suke gabatar da muhawara.

Akawun Majalisar Dokokin Jihar, Barista Umar Yusuf Gital ne ya bayyana wa Aminiya haka a zantawa da shi.

Barista Gital ya ce hurumin majalisar ne kamar yadda yake a tsarin mulkin kasa na 1999 cewa za ta iya amfani da wani harshe bayan Harshen Ingilishi.

Ya ce majalisar ba za ta iya anfani da Harshen Hausa ba sai a farkon zaman majalisar an gabatar da kudiri na dokokin zaman majalisar, inda za a bukaci a amince a rika amfani da Hausar, sannan a amince da shi kafin su fara aiki da shi.

Ya ce idan ba a gabatar da kudirin ba, to, ba za a samu danar yin amfani da kowane harshe ba, bayan Ingilishi.

Barista Gital ya ce wannan shi ya sa idan ana zaman majalisa za ka ji wani zai tashi ya yi magana da Hausa wani kuma ya yi da Ingilishi.

Ya ce amma rahoton zaman majalisa da Ingilishi ake rubuta shi kamar yadda ake yi a kotu, “Saboda haka dokar ta tanada,” ya bayyana wa Aminiya.

Wani tsohon ma’aikacin majalisar, ya ce an fara amfani da dokar ne tun farkon majalisar a 1999, amma kowace majalisa wa’adinta shekara hudu ne, inda ya ce duk bayan shekara hudu idan wata majalisar ta zo za ta fara aiki sai ta sabunta dokokin da ta amince za ta ci gaba da aiki da su, ciki har da na amfani da Hausa.

Ya ce bai taba ganin inda aka yi rahoto ko bayanin yadda zaman majalisar ta kaya da Hausa ba, amma ya ce ya san dan majalisa zai iya rubuta kudirinsa da Hausa ya gabatar a zauren idan yana son yin haka.