✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantar Dutse Model ta shirya gasar wasanni

Makarantar Model International School da ke Dutse ta shirya gasar wasannin motsa jiki don amfanin dalibai da malaman makarantun Jihar Jigawa da nufin zaburar da…

Makarantar Model International School da ke Dutse ta shirya gasar wasannin motsa jiki don amfanin dalibai da malaman makarantun Jihar Jigawa da nufin zaburar da daliba su mike tsaye wajen bunkasa harkokin wasa.

Shugaban Makarantar, Malam Lawan A. Yusuf ya  fadi lokacin da aka gudanar da gasar a ranar Juma’a da ta gabata cewa makarantun sakandare da dama ne suka halarci gasar.

A yayin gasar wasannin an yi  gudun buhu da tseren kwai a cokali da gudun saka zare a allura da tseren mita 100 da jefa mashi da kwallon kwando da sauran guje- guje da tsalle-tsalle.

Cikin makarantun da suka yi nasara akwai makarantar Dutse Capital wadda ta zo ta daya a gudun mita 100 da tseren buhu. Hakan ya sa ta ci lambar yabo ta tagulla da Kofin Zinare.

Yayin da Yellow House ne ya zo na biyu Kuma Green House ya zama zakara a fagen gasar yayin da Dutse Capital ta sake zama ta uku ta samu azurfa a tseren mita 100 ita kuma Makarantar Holding Light ta yi ta biyu.

Sauran makarantun da suka shiga gasar sun hada da Makarantar ’Yan mata ta Unity da ke Gwaram wadda ta samu nasarar cin tagulla a gasar tseren mita 100.

Da yake jawabi a wajen bikin Kwamashinan Ilimi na Jihar Jigawa, Malam Lawan Yunusa Danzomo ya yaba wa Shugaban Makarantar Dutse Capital saboda tunanin da ya yi na shirya gasar, inda ya ce hakan zai kara taimakawa wajen kulla zumunci a tsakanin dalibai kuma dalibai masu sha’awar wasa za su samu damar nuna basirarsu.

Ya ce motsa jiki yana kara lafiyar jiki tare da kara wa yara kaifin basira don haka ya bukaci daukacin makarantun jihar su habaka harkokin wasanni a makarantunsu. Ya ce gwamnati a shirye take ta taimaka wa makarantu da kayan wasa na zamani da nufin inganta harkokin wasanni a daukacin makarantun Jihar Jigawa.