✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantu 16 za su samu kwamfutoci 8,000 a Kaduna

Makarantu 16 a jihar Kaduna za su ci gajiyar kwamfutoci 8,000 domin domin bunkasa ilimi da tattatta bayanai. Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna, Dakta Shehu…

Makarantu 16 a jihar Kaduna za su ci gajiyar kwamfutoci 8,000 domin domin bunkasa ilimi da tattatta bayanai.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna, Dakta Shehu Usman Muhammad ya ce za a raba wa makarantun 16 kwamfutocin, kafin isowar wasu karin kwamfutoci 8,000 a nan gaba.

Da yake jawabin bude taron horaswa kan ilimin tara bayanai da aka shiya wa shugabannin makarantun sakandare da malamai 100, a makaratar Queen Amina, kwamishinan ya ce horon ilimin tattara bayanan zai taimaka wa Ma’aikatar wajen gudanar da ayyukanta cikin sauki tare da bunkasa ilimin baki daya.

Ya ce kwas din zai taimaka wa malaman da shugabannin makarantun su san yadda za su yi amfani da shafin ma’aikatar domin tura mata bayanai.

Dakta Shehu ya kara da cewa amfani da kwamfutoci zai taimaka wa shugabannin makarantu wajen gudanar da aikinsu cikin sauri da sauki, sabanin yadda yanzu ake yin komai a kan takarda.

Ya ce horon ya kunshi koya musu yadda za su hada kwamfutocinsu da wayoyinsu, a yayin da ita kuma ma’aikatar ke lura da kowannensu.

Ya ce, kwamfutoci 8,000 da za a raba wa makarantu 16 sun riga sun iso, amma ana jiran karin wasu 8,000 da za a ba wa wasu makarantu 16.

“Dadin da dawa, za mu bi mataki-mataki domin karfafa makarantun suka samu kwamfutocin ta bangaren tsaro, wutar latarki, karfin layin sadarwa da kuma ma’aikata,” inji shi.

Daga Salisu Salisu Ahmad da Mohammed I. Yaba da Abdulkadir Shehu, Kaduna.