✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarkashiyar tsige Shugaban INEC ta tayar da kura

Tsarin da INEC ta tanada ya sa zai yi wuya a yi magudi a Zaben 2023.

Rahotanni sun nuna cewa akwai wasu kusoshi da ke shirin tumbuke Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu daga kujerarsa.

Lamarin wanda tuni ya tayar da kura na faruwa ne a daidai lokacin da bai wuce  watanni hudu a gudanar da Babban Zaben kasar ba na 2023.

Kusoshin dai Aminiya ta gano na da kusanci da wani mai rike da babban mukami a Abuja, kuma za su ci gaba da kokarin tsige shi daga matsayinsa ne, matukar ba zai yi yadda suke so ba a Zaben 2023.

A nata bangaren, INEC din ta ce ta yi nisa a nata shirin, musamman bangaren samar da kayayyakin zaben, da kuma wadanda za su yi aikin.

Shugaban INEC din a ganawarsa da Aminiya ya jaddada cewa Hukumar za ta yi amfani da na’urar BVAS ne a 2023 din, kamar dai yadda aka gani a da dama daga zabukan cike gurbi da aka yi a wurare daban-daban a Najeriya.

A ranar Laraba ne Gamayyar Kungiyoyin Jam’iyyun Najeriya (CUPP) a taron da suka gudanar da manema labarai a Abuja, sun bayyana damuwa kan wannan yunkuri na tsige Farfesa Yakubu.

Kakakin (CUPP), Ikenga Ugochinyere ya ce baya ga wannan, sun bankado yunkurin da ake yi na hana amfani da tsarin BVAS din, wanda zai dinga watsa sakamakon zaben ta Intanet a lokacin da ake yinsa.

Kafin wannan taro na kungiyar dai, wani jigo da ya nemi a sakaya sunansa, ya sanar da Aminiya cewa tsarin da INEC din ta dauko don yin amfani da shi a 2023, ya sa magudi zai yi wahala.

Manyan sabbin tsare-tsaren da ake dambarwar a kansu sun hada da amfani da na’urar BVAS din domin tantance masu zabe, da cire tsarin amfani da takardun dangwale, da kuma bayyana sakamakon zabe nan take da na’ura.

Binciken Aminiyar dai har wa yau, ya gano wasu Gwamnoni guda biyu – daya daga yankin Arewa maso Gabas – daya kuma daga Kudu maso Gabashin kasar, hadi da wani Shugaban Majalisar Dokokin jiha, da suka hada kai da wadancan kusoshi, domin tsige Shugaban INEC din.

Daga Abdulaziz Abdulaziz da Abbas Jimoh da Rahima Shehu Dokaji.