✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makasudin ficewata daga PDP zuwa NNPP — Kwankwaso

Kwankwaso ya ce PDP ta gaza gane muhimmancinsa a siyasance

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana dalilansa na ficewa daga jam’iyyar PDP tare da sauya sheka zuwa NNPP a ranar Talata.

Kwankwaso, wanda na daya daga cikin mutanen da suka nemi tsayawa takarar kujerar Shugaban Kasa a inuwar jam’iyyar ta PDP a zaben 2019, ya karbi katin zama dan jam’iyyar NNPP a mazabarsa da ke Abuja ranar Talata. inda ya bukaci ’yan Najeriya da su bi bayansa don samar wa kasar canjin da ta ke bukata.

Ya ce sauya shekar tasa ta bude wani sabon babi a siyasar Najeriya, kuma NNPP ce kadai a cikin jam’iyyu ke da abin da za ta iya kai Najeriya ga tudun mun tsira.

Kazalika, ya ce PDP da APC sun gaza biya wa ’yan Najeriya bukatunsu, don haka babu bukatar sake zabensu a 2023.

“Mun samu wani yanayi a watan Afrilun bara, inda aka raba mukaman shiyya-shiyya a tsakanin jihohi kuma an bai wa dukkan shugabannin sauran jihohi shida dama. Amma a Kano wasu na ganin ba ni da muhimmanci don haka suka yi abin da suka ga dama.

“Wannan shi ne makasudin ficewa ta daga jam’iyyar, amma sai da na shafe tsawon shekara daya ina jiran shugabbanin PDP su yi magana da ni a kan lamarin, amma shiru.

“Saboda haka, na fahimci cewar babu yadda za a yi a samu daidaito, duk da yadda muka yi kokarin kaucewa hakan.

“Na karbi katin zama dan jam’iyyata kuma ba shakka, ni ne sabon dan jam’iyyar NNPP. Na ji dadin zama dan jam’iyyar NNPP a Kano.”

A ranar Talata ce Kwankwaso ya aike wa da shugaban mazabarsa na PDP a Kano takardar ficewa daga jam’iyyar.

’Yan gaban goshin Kwankwaso, wato Abba Kabir Yusif da Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo tuni suka bi sahunsa wajen ficewa daga PDP zuwa NNPP a ranar Litinin.