✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mako 2 babu layin sadarwa a Sabon Birni

Layi daya tal da ya rage yana aiki a Karamar Hukumar Sabon Birni mai fama da ’yan bindiga ya katse

An shiga mako na biyu ke nan da katsewar layin sadarwa daya tal da ya rage yana aiki a Karamar Hukumar Sabon Birni da ke fama da hare-haren ’yan bindiga a Jihar Sakkwato.

Wakilinmu ya gano cewa tun bayan dawowar sadarwa a yankin bayan toshewar da Gwamnatin Tarayya ta yi a baya saboda dalilai na tsaro, layin Airtel ne kadai ya ci gaba da aiki a yankin, har zuwa lokacin shi ma ya dauke.

Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Sabon Birni, Muhammad Idris Gobir, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Sati biyu ke nan ake magana ba mu da sadarwa a karamar hukumarmu, muna cikin damuwa sosai, komai ya yanke a wurin.

“An gabatar da korafi ga mahukunta amma babu wani mataki da aka dauka.”

Ya kara da cewa, an dauki tsawon lokaci layukan sadarwa na MTN da GLO ba su aiki a yankin nasu, in ban da layin Airtel kadai.

Ya ce akwai bukatar hukumomin da lamarin ya shafa su yi abin da ya kamata domin jama’arsu na bukatar yin rayuwa kamar kowa, sabanin yadda aka kyale su da ’yan bindiga sai yadda suka yi da su.

Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “’yan bindiga ne suka kona kayan aikin sadarwa na Airtel don ba su damar ci gaba da cin karensu babu babbaka, abin da ya haifar da matsalar ke nan.”

Kazalika, wata majiya daga kauyen Kurawa wadda ita ma ta bukaci a sakaya sunanta, ta fada wa wakilinmu cewa, “Daukewar sabis din MTN da  GLO da kuma Airtel ya bai wa barayi damar shiga yankinmu.

“Muna cikin rashin sabis kuma ’yan bindiga suna cin karensu babu babbaka.

“Makon da ya gabata sun (’yan bindigar) shigo Kurawa sun kwashi mata bakwai, haka shekaranjiya sun shiga garin Fillo sun kwashi mata uku, wanda a nan ne aka yi dauki-ba-dadi tsakaninsu da mutanen gari aka samu nasarar harbe biyu daga cikinsu, yanzu haka suna hannun jami’an Gatawa amma guda ya rasu.

“Ba mu san dalilin da ya sa aka rufe mana sabis ba, duka layukan sadarwa a yankin ba su tafiya.

“Barayin sun dauki mutum bakwai a Garin Zago Kurawa, uku a Kwaren Gamba sannan uku a Tarah, kuma sun cinye mana gonaki.”

Ya zuwa hada wannan rahoton, kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin Shugaban Karamar Hukumar Sabon Birni, Ummaru Dan Yaro, hakan ya ci tura.

Yankin Sabon Birni a Jihar Sakkwato na daya daga cikin wuraren da ayyukan ’yan ta’adda suka munana, wanda kawo yanzu an kashe mutane da dama an kuma yi garkuwa da daruruwa a yankin.