✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mako mai zuwa za a sake bude makarantu a Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce babu makawa za ta sake bude makarantun jihar ranar 18 ga watan Janairu, 2021. Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Aliyu…

Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce babu makawa za ta sake bude makarantun jihar ranar 18 ga watan Janairu, 2021.

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Aliyu Tilde, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata ya kuma ce daukar matakin ya biyo bayan amincewar Majalisar Zartarwa ta Jihar.

Aliyu Tilde ya ce tun da a samu ko da mutum daya da ke dauke da cutar COVID-19 a makarantun jihar ba, babu dalilin da zai sa a ci gaba da rufe makarantun.

Ya ce, “Shekarar karatu ta 2020/2021 za ta fara a wannan rana. Muddin ba mu tashi tsaye mun daina tsoron cutar COVID-19 ba, to tabbas za ta dagula karatun yara baki daya, kamar yadda ta yi wa zangon karatu na 2019/2020.

“Saboda haka, ya kamata iyaye, malamai, dalibai da ma sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi su yi amfani da wannan sanarwar,” inji shi.

Ya kuma ja hankulan makarantun kan su ci gaba da daukar matakan kariya kamar yin amfani da kyallen rufe fuska, bayar da tazara, tsaftar muhalli da kuma yin gwaji a kai a kai, amma ba a sake rufe makarantu ba, sai dai in ya zama babu makawa.

A baya-bayan nan ne dai dawowar cutar a karo na biyu ya tilasta sake rufe makarantun a karo na biyu a jihohi da dama ciki har da Bauchin domin guje wa yaduwar cutar.

Ya zuwa ranar Talata dai, mutum 1,093 ne aka tabbatar da kamuwarsu da cutar a Jihar, 17 kuma suka mutu, yayin da 945 kuma suka warke, kamar yadda alkaluman Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) suka nuna.