✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makomar ilmin firamare a Jihar Kaduna

An fara ganin alamun kawo karshen takaddamar da ta shiga tsakanin Gwamna Nasir el-Rufa’i da malaman makarantun  Firamare domin kuwa an ce an janye yajin…

An fara ganin alamun kawo karshen takaddamar da ta shiga tsakanin Gwamna Nasir el-Rufa’i da malaman makarantun  Firamare domin kuwa an ce an janye yajin aikin da kungiyar malaman makarantun  ta yi kwanaki goma tana yi tare da goyon bayan kungoyoyin kwadago na kasa don nuna rashin amincewarsu da abin da suka kira danyern kai wajen korar wasunsu sama da dubu ashirin da daya daga bakin aiki bisa zargin rashin cin jarrabawar da  ake yi wa ‘yan aji hudun da suke koyarwa. 

A ranar Litinin da ta gabata an fara koyarwa a makarantu a wani yanayin da masu lura da yadda  al’amura ke gudana suka bayyana da cewa  barin da aka kasa kwashewa duka.  Wasu daga cikin iyayen yaran da suka kagara su ga karshen  salular da suke gani ana  yi wa sha’anin ilmi a Jihar Kaduna  sun daure sun tuttura ‘ya’yansu makaranta, wasu tsiraru daga cikin malaman kuma, musamman wadanda aka ce sun cinye waccan jarabawar da aka yi sun hallara ilahirinsu, amma sai dai haka nan aka yi ta koyar da rabin dalibai a wasu ajujuwa, wasu ajujuwan  kuma ga dalibai nan a ciki amma ba malaman da za su koyar.  Haka nan dai aka ci gaba da sha’ani wasu na cewa akwai sauran rina a kaba, domin kuwa tun can da farkon-fari ma kungiyar malaman ba ta bi ka’odojin janye yajin aikin ba, kuma kaman yadda  wasu ke cewa ba a bi ta kan kungiyar kwadago ba kafin bayar da sanarwar janye yajin aiki, ba a kuma ce ga inda gwamnati ta zauna da kungiyar malaman ba don sasantawa  kafin a kai ga haka.  Baicin haka nan kuma kungiyar malaman ba ta ce uffan ba game da wata kara da ta shigar kotun ma’aikata  game da jayayyar da ke tsakaninta da gwamnatin jihar Kaduna sakamakon korar wasunsu da ta yi. Wannan janye yajin aiki shi ake kira cuku-murdi, domin kuwa ana iya cewa har yanzu tana kasa tana dabo ke nan . 

Abin da kawai aka ce ya bugawa kungiyar malaman kaimi har ta kai ga cewa ta janye yajin aikin shi ne batun da gwamnatin Jihar Kaduna ta sha nanatawa cewa za a ba dukkan malaman makarantun  da aka rigaya aka jefa a mala daman sake daukan jarabawa irin waccan ta farko, wanda kuma ya samu makin da ake bukata za a koma da shi kan aikinsa. Irin waccan jarrabawar ce kuma aka ce wai wasu  masu sha’awar aikin malanta, sama da dubu arba’in da uku sun rubuta don maye gurbin wadancan sama da dubu ashirin da daya da aka rigaya aka rarraba wa wasunsu takardun sallama.  

To a yanzu gwamnati ta ce daga lokacin da ta bayar da waccan shelar ta sake bayar da dama ga  wadancan korarrun malaman don rubuta wata jarrabawar, kuma wai an ce an samu  guda dubu goma sha biyu daga cikinsu  da suke son sake komawa bakin aikinsu, kuma daga cikinsu akwai wadanda takardun sallamarsu daga aiki ta dade da nuna a  hannayensu.

To, a daidai wannan lokacin ne kuma gwamnati ta bayar da sanarwar cewa  daga cikin wasu guda dubu arba’in da uku da wai suka zauna jarabawa don daukanrsu aiki a makwafin wadancan korarrun guda dubi ashirin da daya, ta tantance wasu dubu ashirin da hudu da za a yi wa intabiyu (ganawar daukar aiki) daga Larabar nan a matsayin wadanda za su canji wadancan dakikan da aka sallama. Gwamnati ta ce tana so ne ta tantance adadin wadanda take bukata guda dubu ashirin da biyar daga cikinsu domin su fara aiki a watan Fabrairun da za a shiga, tun da dai ta nuna  cewa babu gudu ba kuma ja baya game da korar wadancan takkwalayen da kuma maye gurbinsu da wa su sababbin hazikai.  Idan kuwa haka ne ina makomar wadancan dubu goma sha biyu daga cikin korarrun malaman sama da dubu ashirin da daya idan har sababbin malaman suka fara aiki?  Gwamnati za ta kuwa iya  ci gaba da tantance wasu daga cikin korarrun, ta kuma hada su da wadancan sabbin  a ci gaba da tafiya a haka? Tana da halin biyan sababbin malaman makudan kudaden da suka fi wadanda ake biyan malaman da aka kokkora, sa’annan kuma ta kara da wasu dubbai daga cikin wadanda aka gama yi wa tereren tsiya, an kuma gaya wa duniya cewa su makiyan ‘ya’yan talakawan da suke koyarwa ne, domin babu wani abin kirkin da suka nakalta a harkar koyarwa, ba su kuma da wani tasiri a tsarin inganta harkokin ilmi irin na Gwamna Nasir? To idan har an mayar da wasunsu bakin aiki tatsuniya ce za su koya wa dalibai ko kuwa?

Dangane da haka ana iya cewa kai dai kawai a yi sha’ani, wai an cuci na kauye. Shigo-shigo ba zurfi ne ake ganin an yi wa wadancan korarrun malaman da sunan sake neman komawa bakin aiki. Da zarar an mimmika wa sababbin da ake son dauka takardu  za a fita batunsu ne kawai, idan kuma suka na ce da bibiyar sakamakon jarabawar da za a sa sake zanawa babu wanda zai waiwaye su, haka nan za su gaji da bilinbituwa  su  kuma rungumi kaddara  bayan sun gama ragaita da tagayyara.  

Yanzu dai ba a ce  kada wani korarren malami ya nemi komawa bakin aikinsa ba, amma abin da ake gani shi ne mafi a’ala game da makomarsa shi ne hanzarta biyansa zufar goshinsa tun kafin ya gama tsanewa ta yadda zai kama gabansa, ya  bidi  wata sana’ar da Gwamna Nasir ya ce gwamnatinsa a shirye take ta kyautata musu dangane da haka. 

To amma wanda duk ya ce zai ba ka riga sai ka kalli ta wuyansa. Idan da gaske ne korar wadancan malamai sama da dubu ashirin da daya da kuma  hazikan da za a dauka, dubu ashirin da biyar da niyyar inganta  ilmin ‘ya’yan talakawa ne to sai a hanzarta a warware duk wata tangarda da za ta iya tasowa game da daukar wadancan hazikan malaman, a kuma tabbatar sun fara aiki gadan-gadan ba tare da  fuskantar wani cikas ko afkawa cikin wani halin matsi ba, sa’annan kuma su wadancan korarrun a samar da wadatattun kudden da za a sallame su farat daya, ya zamanto ba kare bin damo. Ta haka ne za  shar don a sha da karari, gwamnati ta dukufa wajen inganta ilmi a tsanake, hankulan dalibai da iyayensu kuma su kwankwanta.  

Muddin aka kasa samun nasara a wadancan matakai guda biyu, to fa sha’anin ilmi a Jihar Kaduna zai ci gaba da gamuwa da tangardar da ta samo asali tun farkon kafuwar wamnatin Malam Nasir, kuma haka zai janyo koma bayan ilmi a Jihar Kaduna fiye da na sauran jihohin kasar nan. A yanzu dai ya kamata Gwamna Nasir ya tabuka wajen fahimtar da jama’a cewa shi fa aniyarsa ta daukar matakan da suka ki ci suka ki cinyewa don farfado da martabar ilmi a jiharsa ita ce kyautata wa ‘ya’yan talakawa, amma ba muzanta sha’anin ilmi da harkokin koyarwa ba idanun sauran ‘yan Najeriyan da ake nuna musu cewa har yanzu dai jahilci ya yi wa al’ummomin Jihar Kaduna katutu, domin hatta ingantattun malaman Firamare ma babu na amincewa. Ta haka ne kawai za a tabbatar da dorewar aikin malanta a makarantun Firamaren Jihar Kaduna