✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malam bude mana littafi: Kwaron da ke bad-da kama ya yi kama da maciji

Rayuwar kwaron takaitacciya ce

Malam-bude-littafi na daya daga jerin kwari masu tashi, kuma akwai su nau’i daban-daban.

Game da rayuwar dabbobi na wannan makon, a takaice, bari mu kalli rayuwar daya daga cikin nau’in malam bude mana littafi wanda a Turance ake kiransa da suna ‘Atlas Moth’.

Atlas shi ne mafi girma daga nau’ikan malam bude mana littafi da ake da su a fadin duniya. Fadin fuffukensa ya zarce na tafin hannun mutum.

Galibi, an fi samun Atlas ne a dazuzzukan nahiyar Asiya, musamman a kasashen China da Bangladesh da Cambodia da Hong Kong da Indiya da sauransu.

Kwaro ne mai ado da zane birjik a jikinsa.

Adon jikinsa akwai daukar ido da kuma ban tsoro, saboda wasu lokutan zanen jikinsa na kama da kan maciji.

Sai dai kuma, duk da girman wannan kwaro, ba ya iya cin abinci yadda ya kamata, kuma rayuwarsa takaitacciya ce.

Sukan yi amfani da siffar maciji da suke da ita wajen bad-da kama don kare kansu daga cutarwa.

Duk lokacin da suka tada fuka-fukansu, sukan hade su wuri guda, daga nesa za a zaci maciji ne.

Don haka sukan yi amfani da wannan baiwa ta musamman da suke da ita wajen tsoratar da duk abin da ya zo don cutar da su.

Duk lokacin da manyan kwari suka kawo masa farmaki, sai ya sarrafa fuka-fukansa su dauki kamanni irin na kumurci.

Bayan haka, sai ya soma jan jikinsa a hankali ya rika kwaikwayon maciji. Ta haka yake razana masu farautarsa, kamar tsuntsaye da kadangaru da sauransu.

Malam-bude-littafi (Atlas Moth)

Haka nan, kwaron na da wasu zane-zane masu kama da ido a jikin fuka-fukan nasa. Su ma sukan taimaka masa wajen razana masu farautarsa.

A bangaren mu’amalar mata da miji kuwa, Atlas Moth kan shafe sa’a 24 manne da juna yayin saduwa.

Bayan saduwar, macen kan saka kwai kimanin 150 ko makamancin haka, sannan ta mutu bayan haka.

Rayuwar wannan kwaro ta ‘yan makonni ce kafin ya mutu.