✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malamai sun yi bore kan kin biyan su albashin wata biyar

Malaman firamare a Nasarawa sun yi bore kan kin biyan su albashin wata biyar.

Malaman makarantun firamare sun yi zanga-zanga kan rashin biyan su albashin wata biyar a Jihar Nasarawa.

Dandazon malaman na Karamar Hukumar Keffi, dauke da kwalaye, sun tare Sakatariyar Karamar Hukumar, suna neman Shugaban Karamar Hukumar ya yi musu bayani kan kin biyan su hakkokin nasu.

“Sun kwashe awanni suna jiran Shugaban Karamar Hukumar ya yi musu jawabi amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.

“Bayanin da na samu shi ne a tsawon wata biyar din, wani kaso kawai ake biyan su na albashin nasu,” inji  wani jami’in Karamar Hukumar da ya bukaci a sakaya sunansa.

Daruruwan malaman na zargin Karamar Hukumar da rashin adalci da kuma yin biris da halin da suke ciki a tsawon wata biyar din.

Shugaban Kungiyar Malamai ta Kasa (NUT), Reshen Jihar Nasarawa, Francis Tete, ya ce ba a sanar da kungiyar game da zanga-zangar ba a hukumance.

Amma ya ce Kungiyar za ta dauki mataki nan take domin shawo kan matsalar, kuma tun da farko ta tattauna da malaman domin lalubo bakin zaren.

“Mun yi zama da malaman jiya inda muka yi zuzzurfan tattaunawa kan hanyoyin magance matsalar,” inji shi.