✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malaman jami’o’i sun shiga wani hali —ASUU

Muna cikin matsala sosai sakamakon 'bakin talaucin' da muka shiga.

Wasu daga cikin malaman jami’o’i a Najeriya sun shiga harkokin noma da sauran sana’o’i domin neman na abinci a yayin da yajin aikin kungiyar malaman jami’o’in kasar (ASUU) ya ki ci ya ki cinyewa.

Tun a ranar 14 ga watan Fabraitun da ya gabata ne ASUU ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamnatin Tarayya na tsawon wata guda, sai dai daga baya kungiyar ta mayar da yajin aikin na sai abin da hali ya yi.

Da yake zantawa da Jaridar Punch, Shugaban Kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce, matakin da gwamnati ta dauka na kin biyan bukatun kungiyar yana cutar da al’ummar kasar.

“Saboda haka malamai da yawa suna barin aikin sun koma yin noma da sauransu; Malaman jami’o’in sun gaji da yadda gwamnati take yi masu don haka, suke neman mafita. Don haka da yawa ma za su fice ko bayan yajin aikin,” in ji shi.

A ranar Asabar din da ta gabata ne Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU) da Kungiyar Ma’aikata na jami’o’i da na Cibiyoyin Ilimi (NASU) suka dakatar da yajin aikin da suke yi bayan da Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin biyan Naira biliyan 50 na kudaden alawus-alawus na ma’aikatan jami’o’in da suka hada da ’yan Kuniyar ASUU.

Sai dai ana sa ran za a takaita ayyukan a jami’o’in gwamnati ganin cewa ASUU na ci gaba da yajin aiki.

Ministan Ilimi na Najeriya, Adamu Adamu ya ce ASUU ta ki amincewa da kudirin gwamnati kan dokar “ba aiki, babu albashi”.

Kungiyar ta dage cewa dole ne gwamnati ta biya malaman albashinsu na tsawon watanni shida da suka shafe suna yajin aiki da a ba biya su ba.

‘Mun shiga wani hali’

A tattaunawar da BBC ta yi da wasu daga cikin malaman jami’o’in, wasu daga cikinsu sun bayyana cewa suna cikin matsala sosai sakamakon ‘bakin talaucin’ da suka shiga.

Wasu kuma sun bayyana cewa lamarin da sauki ba kamar yadda ake ruruta shi ba.

Malam Aminu Makama, wanda malami ne a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, ya shaida wa BBC cewa suna cikin wani hali.

Ya bayyana cewa sakamakon wannan yajin aikin, da dama sun fara sana’o’in da bai kamata a ce malamai suna yin irin su ba.

“Na san malamin da yake aikin feshi a gonakin mutane kuma babban malami ne wanda yake da digirin-digirgir” in ji Malam Aminu.

“Akwai wadanda wallahi manyan malamai ne amma sun soma sayar da kayayyakin gidansu, kamar irin su talabijin da injin wanki da abubuwan yau da kullum saboda su tafiyar da gidansu.

“Akwai malaman da ‘ya’yansu da yawa ba sa zuwa makaranta saboda ba su samu damar da za su biya kudin makaranta ba, kuma makarantun ba za su saurara musu ba.”