✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalejojin kimiyya da fasaha sun janye yajin aiki

ASUP ta dakatar da yajin aikin da ta shafe kwana 65 tana gudanarwa.

Kungiyar Malaman Kwalejojin Kimiyya da Fasaha ta Najeriya (ASUP)  ta dakatar da yajin aikin da ta shafe kwana 65 tana yi.

Kakakin ASUP, Abdullahi Yalwa, ne ya sanar da janyewar a ranar Laraba.

Ya ce an janye yajin aikin ne bayan bitar rahoton Kungiyar kan aiwatar da yarjejeniyar da ta kulla tsakaninta da Gwamantin Tarayya kan bukatunta.

ASUP ta ce rahoton ya nuna Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da yarjejeniyar kamar yadda aka yi alkawari a tsakanin bangarorin.

Amma ya ce kungiyar ta dakatar da yajin aikin ne na wata uku domin ba wa gwamnatin damar kammala aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla.

Ya ce ASUP na umartar daukacin mambobinta a su koma bakin aiki daga ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni, 2021, duba da rokon da al’umma da Majalisar Tarayya da kuma iyayen kwalejojin suka yi musu.

Abdullahi Yalwa ya ce kungiyar ta gamsu da dokar da aka yi na soke bambanci tsakanin Digiri da Babbar Difloma ta Kasa, kafa majalisun gudanarwar kwalejojin da kwamitocin ziyarar gani da ido kan gyara kwalojin.

A cewarta, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta tabbatar mata cewa ana aikace aikacen ganin an saki kudade domin ayyukan gyaran.

A ranar 6 ga Afrilu, 2021, malaman suka fara yajin aikin sai abin da hali ya yi, sai gwamnati ta biya bukatunsu na gyara kwalejojin.

Sun tsunduma yajina ikin ne bayan kimanin mako biyu da cikar wa’adin da suka ba wa gwamnatin.