✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malaman makaranta sun fara yajin aiki a Ingila kan karin albashi

Sun ce dole albashinsu ya dace da yanayin hauhawar farashin kaya

Malaman makaranta a Ingila da yankin Wales sun sanar da tsunduma yajin aiki daga watan Fabrairu mai zuwa saboda karin albashi.

Kungiyar malaman mai suna (NEU) ta ce mambobinta sun amince da gagarumin rinjaye a fara yajin aikin har sai an yi musu karin da zai yi daidai da yanayin hauhawar farashin kayayyaki a kasar.

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin ma’aikatan gwamnatin kasar da dama ke guna-guni kan karancin albashi.

“Mun tabbatar gwamnati ta san akwai bukatar a gyara albashin malaman makaranta,” in ji Kevin Courtney, Babban Sakataren NEU, yayin wani taron kungiyar da aka watsa kai tsaye.

Shugabannin kungiyar dai na shirin ganawa da Ministan Ilimin kasar ranar Laraba.

Shi ma wani Sakataren kungiyar, Mary Bousted, ya ce, “Sun san ba da wasa muke ba. Da gaske muke yi wajen kokarin kare ayyukanmu.”

Kungiyar dai ta sanar da fara yajin aikin ne daga ranar daya ga watan Fabrairu mai zuwa, sannan za ta shafe kimanin kwana shida tana yin yajin aikin a matakan yankuna a watan Fabrairu da Maris masu zuwa.

Sai dai ta ce kowacce makaranta yajin aikin zai shafe ta ne na tsawon kwana hudu.

Ko a cikin makon nan a Ingila da Wales da Arewacin Ireland, ana sa ran ma’aikatan lafiya na Nas-nas ake sa ran su dawo yajin aikinsu a ranakun Laraba da Alhamis.