✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malaman ‘Poly’ sun janye yajin aiki

Malaman kwalejin kimiyya da kare-kere sun janye yajin aikin da suka ta tsundumna na mako biyu. Kungiyar malaman kwalejojin ta ASUP ta bukace su da…

Malaman kwalejin kimiyya da kare-kere sun janye yajin aikin da suka ta tsundumna na mako biyu.

Kungiyar malaman kwalejojin ta ASUP ta bukace su da su koma bakin aiki daga ranar Litinin, 30 ga watan Mayu, 2022.

Da yake sanar da janye yajin aikin, kakakin ASUP, Abdullahi Yalwa, ya ce sun yanke shawarar janye yajin aikin ne a taron Kwamitin Zartarwar kungiyar, inda suka tattauna ka bukatun kungiyar da ya sa suka shiga yajin aikin.

A cewarsa, gwamnati ta biya hudu daga cikin bukatunsu tara da suka gabatar mata, shi ya sa skue ganin dacewar janye yajin aikin.

A cewarsa, za su dakatar da yajin aikin ne domin ba wa gwamnatin tama da kuma lokacin yin abin da ya dace game da ragowawr bukatun malaman kwalejojin.