✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malamin cocin da aka dakatar ya lashe zaben fid-da-gwanin APC a Binuwai

Daga cikin wadanda malamin cocin ya kayar har da tsohon Shugaban PDP

Wani malamin addinin Kirista da aka dakatar daga cocinsa, Rabaran Fada Hyacinth Alia, ya lashe zaben fid-da-gwani ya zama dan takarar Gwamnan APC a Jihar Binuwai.

Rabaran din, wanda babban malamin ne na darikar Katolika a yankin Gboko, ya kayar da mutum 12 a hanyarsa ta zama dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar ta APC.

Daga cikin wadanda malamin cocin ya kayar har da tsohon Shugaban PDP Sanata Barnabas Gemade, da tsohon Ministan Shari’a Michael Aondoaka da tsohon Mataimakin Gwamna Steven Lawani da kuma dan Majalisar Wakilai Hemen Hembe.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa tun kafin zaben fid-da-gwanin da aka gudanar a ranar Asabar dai, Bishop na Katolika a Yankin Gboko, Mos Rabaran Williams Avanya, ya dakatar da Rabaran Alia daga cocin saboda shigarsa harkokin siyasa.

Ba wannan ne karo na farko ba da ake samun manyan malaman addinin Kirista suna shiga siyasa a Jihar Binuwai.

Ko a shekarar 1992 ma, an zabi Rabaran Fada Moses Adasu a matsayin Gwamnan Jihar ta Binuwai.

Rabaran Alia, a cewar shugaban kwamitin zaben, ya samu kuri’a 526,807 ne, lamarin da ya ba shi damar kayar da sauran masu sha’awar tsayawa.

Wanda ya zo na biyu a zaben shi ne Dokta Mathias Ibyuan wanda ya samu kuri’a 113,816 yayin da Dokta Sam Ode ke bin shi da kuri’a 79,369.

Shi kuwa Cif Stephen Lawani ya zo na hudu ne da kuri’a 46,882, Michael Aondoakaa kuma na rufa masa baya da kuri’a 24,596.

Sauran su ne Fasto Terwase Orbunde wanda ya tashi da kuri’a 12,446, da Sanata Barnabas Gemade mai kuri’a 2,365, da Barista Hemen Hembe wanda ya tsira da kuri’a 2473, sannan Mista Godwin Tyoachimin kuri’a 1,228, sai kuma Farfesa Terhemba Shija mai kuri’a 1,048.