✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Malaysia ta ba jakadun Koriya ta Arewa sa’o’i 48 su fice daga kasarta

Dangantaka dai tsakanin kasashen biyu ta dada yin tsami tsakanin kasashen guda biyu.

Kasar Malaysia ranar Juma’a ta mayar da kakkausan martani ga matakin da Koriya ta Arewa ta dauka na yanke huldar jakadanci da ita ta hanyar umartar dukkan ma’aikatan jakandancin kasar da su fice mata daga kasa cikin sa’o’i 48 masu zuwa.

Huldar jakadancin dai ta kazance ne bayan an damke wasu ’yan kasar ta Koriya ta Arewa sannan aka mika su ga kasar Amurka wacce take nemansu ruwa jallo.

“An kama Mun Chol-myong wanda ya ke zaune a Malaysia a shekarar 2019 bayan zarginsa da hada baki wajen zambar kudade da kuma karya dokokin Majalisar Dinkin Duniya,” inji Ma’aikatar Harkokin Wajen Malaysia a cikin wata sanarwa.

Kamawa tare da damka mutanen nata ga Amurka ne ya hassala Ma’aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Arewan ta sanar da daukar tsauraran matakan bisa abin da ta kira laifin da ba za ta taba yafewa ba.

Sai dai Ma’aikatar Harkokin Wajen Malaysia ta bayyana matukar takaicinta da bisa daukar matakain wanda ya kai ga tabarbarewar dangantakar.

“Malaysia na Allah wadai da wannan mataki wanda koma baya ne ga mutunta juna da kuma girmamamawa ga dangantakar kasa da kasa,” inji sanarwar.

Ma’aikatar dai ta ce ta ba dukkan ma’aikatan ofishin jakadancin Koriya ta Arewa da ke birnin Kuala Lampur sa’o’i 48 da su fice daga kasarta.

Kazalika, ita ma Malaysia ta ba da umarnin rufe ofishin jakadancin nata dake Pyongyang, wanda dama aka dakatar da shi tun shekarar 2017 tun bayan kisan wani dan uwan shugaban Koriya ta Arewan, Kim Jong Un a filin jirgin sama na Kuala Lampur.

Dangantaka dai tsakanin kasashen biyu ta dada yin tsami tsakanin kasashen guda biyu.