✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Maleriya da ba a yi magani ba na kawo matsalar kwakwalwa’

Wani masanin kiwon lafiya, John Tobias, ya bayyana cewa barin cutar zazzabin cizon sauro ba tare da an magance ta ba na haifar da matsalar…

Wani masanin kiwon lafiya, John Tobias, ya bayyana cewa barin cutar zazzabin cizon sauro ba tare da an magance ta ba na haifar da matsalar kwakwalwa ga dan Adam.

John Tobias wanda shi ne Kodinetan Hukumar Yaki da Cutar AIDS ta Kasa reshen Arewa maso Gabas, ya yi gargadi cewa cutar na yin kisa muddin ba magance ta ba.

“Zazzabin cizon sauro na iya lalata kwakwalwa da daukewar aikinta idan har ta kai matakin cutar anaemia ko tara jini, wanda ke kawo matsala ga kwakwalwa.

“Tana kuma kawo matsala mai alaka da karancin gudanar jini zuwa kwakwalwa, saboda idan gudanar jini ya yi karanci, ba zai iya tura adadin da kwakwalwa ta yi aiki yadda ya kamata ba.

“Daga nan dole mutum ya samu matsala, kwakwalwarsa ta fara aiki ba daidai ba.

“Da zarar an kai wannan mataki, to abin ya yi tsanani, mutumin zai rika tabu, ya rika abubuwa na rashin hankali saboda kwakwalwarsa ta samu matsala.’’

Ya bayyana cewa gargadin ya zama wajibi lura da karancin wayar da kan jama’a game cutar da hadarinta da mtsalolin da take haifarwa da kuma yadda take rugurguza garuwar jikin dan Adam.

Don haka ya yi kira ga masu cutar ta zazzabin cizon sauro da su “hanzarta neman magani domin cuta ce mai barazana ga rayuwa.

Jami’in na hukumar NACA ya bayyana cewa cutar maleriya hanya ce ta shigar cututtuka jikin dan Adam, irin su HIV, tarin fuka da COVID-19.

Don haka yaka ya jaddada muhimmancin daukar matakan kariya da kuma magance ta.

Don haka ya ba da shawarar hanzarta yin yin gwaji kafin shan maganin, maimako yin gaban kai.

Ya ce yadda yawancin mutane ke yin gaban kansu wajen yin maganin cutar ba tare da an yi musu gwaji be kuskure ne.

“Akwai kwayoyin cuta daban-daban har guda biyar da kowannensu ke haddasa cutar.

“Dole sai an yi gwaji a gano kwayar da ta haddasa irin malariyar da mutum ke fama da ita da kuma maganin da ya dace da ita domin samun cikakkiyar waraka.”

Don haka ya yi kira ga kungiyoyin fararen hula da su dage wajen wayar da kan jama’a kan illolin da tattare da cutar.

Hukumar Lafiya ta Dunya (WHO) ta bayyana cewa cutar zazzabin cizon sauro na yin kisa, kuma ana kamuwa da ita ne sakamakon cizon macen sauro nau’in anophele.

WHO ta ce akalla mutum miliyan 241 ne ke fama da cutar a duniya kuma ta yi ajalin mutum 627,000 a 2020.

Kafin nan, a 2029 mutum miliyan 14 ne ke fama da cutar wadanda da ga cikinsu ta yi ajalin 558,000.