✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mali: Mutumin da ya kusa kashe Shugaban kasa ya rasu

Gwamantin Mali ta sa a gudanar da bincike kan rasuwar maharin a hannun hukuma.

Mutumin da ya yi yunkurin kashen shugaban rikon kasar Mali, Kanar Assimi Goita, ya rasu a inda ake tsare da shi.

Gwamnatin Mali ta ce mutumin ya mutu ne a ranar Lahadi a yayin da ake gudanar a bincike kan yunkurinsa na caka wa shugaban kasar wuka.

“A yayin da ake ci gaba da bincike… rashin lafiyarsa ta tsananta” har aka kwantar da shi a asibiti, “amma ya rasu,” inji sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar.

Sanarwar ta ce an bayar da umarnin gudanar da bincike domin a gano musabbabin mutuwar mutumin.

A ranar Talata, mutumin, wanda ba a bayyana ko wane ne ya yi yunkurin caka wa Kanar Goita wuka a Babbar Masallacin da ke birnin Bamako, inda shugaban ke halartar Sallar Idin Babbar Sallah.

Bayan harin, jami’an tsaro sun hanzarta dauke shugaban, daga baya ya sanar cewa yana cikin koshin lafiya.

Shi kuma maharin, wanda ke sanye da wandon jins da farar riga, aka cukuikwiye shi aka yi awon gaba da shi.

“Yana daga cikin hadarin da ke tattare da zama shugaba, za ka yi ta fuskantar barazana. A kowane lokaci akwai masu neman tayar da zaune tsaye,” inji Kanar Goita.