✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mali ta yi wa sojojin Cote d’ivoire 49 afuwa

Mali ta fita daga sahun kasashen da ake iya razanawa.

Shugaban Gwamnatin Mali Kanar Assimi Goita ya yi afuwa wa sojojin nan na Cote d’ivoire 49 bayan da a karshen makon jiya wata kotun kasar ta yanke wa kowanensu hukuncin zaman gidan yarin shekaru 20.

Kakakin gwamnatin rikon kwaryar Mali Kanar Abdoulaye Maiga ne ya bayyana hakan yayin zantawa da Gidan Talibijin na ORTM a daren ranar Juma’a.

Bayanai sun ce kotun dai ta tuhumi sojojin da aka yi wa afuwa da shiga kasar ba kan ka’ida ba da nufin tayar da zaune tsaye, yunkurin juyin mulki da wasu tarin laifuka masu nasaba da haddasa rudani.

Matakin kama wadannan sojoji ya haifar da tankiyar diflomasiya a tsakanin kasashen biyu makwaftan juna, a yayin da CEDEAO ta umurci Mali ta gaggauta sakin su ko kuma ta dauki matakin ladabtarwa akanta.

Sai dai a sanarwar da kakakin gwamnatin ya bayar ya ce suna jaddada wa shugaban rikon kungiyar ECOWAS wato Shugaban Guinea Bissau Embalo Sissoko cewa, tun a ranar 14 ga watan Janairun 2022 Mali ta fita daga sahun kasashen da ake iya razanawa domin tun wannan rana kasar ta samu cikakken ‘yancin kanta, furucin da Nassirou Saidou ke ganinsa tamkar na yaudara.

A ranar 10 ga watan Yulin 2022 ne hukumomin Mali suka cafke sojojin na Cote d’ivoire 49 jim kadan bayan saukarsu a filin jirgin saman Bamako.

Hukumomin sun zargin sojojin da shiga kasar ba da izini ba, da kuma zargin sun je ne da zummar shirya wata makarkashiya a cewar kasar ta Mali, yayin da hukumomin Cote d’ivoire ke cewa dakaru ne da aka tura don ayyukan zaman lafiya a karkashin Majalisar Dinkin Duniya.

Sojojin sun isa gida

Ya zuwa yanzu dai tuni sojojin wadanda suka shafe kimanin watanni shida a tsare sun isa birnin Abidjan a Yammacin jiya Asabar.

Wata majiya ta ce, kafin isa birnin Abidjan, sojojin sun yada zango a kasar Togo domin ganawa da Shugaba Faure Gnasingbe wanda ya shiga tsakanin domin warware wannan takaddama tsakanin Mali da Cote d’Ivoire.

Yayin da isarsu a birnin Abidjan kuwa, Shugaba Alassan Ouattara ya gana da sojojin, tare da jinjina wa kokarin da kasashe aminai suka yi domin ‘yantar da wadannan sojoji.

Hakazalika, Ouattara a jawabin nasa, ya bayyana Mali a matsayin kasa aminiya ga Cote d’Ivoire.