✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mamakon ruwan sama zai hana jirage tashi —NIMET

An yi hasashen za a shafe kwana uku ana tafka mamakon ruwan sama.

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NIMET) ta sake hasashen samun mamakon ruwan sama mai karfin gaske a sassan kasar daga ranar Talata zuwa ranar Alhamis.

A hasashen yanayin da ta fitar a ranar Litinin, hukumar ta ce a cikin lokacin, za a iya samun ruwan sama mai yawa a jihohin Bauchi, Jigawa, Kano, Katsina, Zamfara, Kaduna, Kebbi, Sokoto da kuma Neja.

Ana kuma sa ran samun ruwan sama matsakaici a jihohin Yobe, Kwara, Ogun, Osun, Ondo, Legas, Edo, Delta, Taraba, Adamawa daga ranar Talata, Laraba da kuma Alhamis.

Sauran su ne jihohin Ekiti, Filato, Nasarawa da Binuwai, Enugu, Ebonyi, Anambra, Abiya, Imo, Kuros Riba da Akwa Ibom.

NiMet ta ce akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwa musamman a jihohin da ake sa ran samun mamakon ruwan, hakan kuma ka iya haifar da karyewar gadoji, rushewar gidaje da kuma hana tashin jirage.

Ana kuma na iya kawo tasgaro ga harkokin tafiye-tafiye da kuma sururi a fadin jihohin.

Aminiya ta ba da rahoton cewa ruwan sama yawanci yana shafar sufurin jirage wanda ke haifar da jinkiri ko hana tashin jirgi baki daya.

“Don haka, an shawarci jama’a da su yi taka-tsantsan, su guji wuraren da ba su da kasa da ruwa mai gudana,” inji hasashen.

Ta kuma ba da shawara ga jama’a da su kasance cikin shiri don gujewa lahani daga hadarin da ke tattare da ruwan saman.