✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mamu ya yi wa matar liman ciki

Ana zargin mamun ya mayar da matar limamin sa-dakarsa.

Limamin wani masallaci a Jihar Oyo ya kai karar wani mamun masallacinsa a gaban kotu yana zargin mamun da yi wa matarsa ciki.

Limamin mai suna Alhaji Lukman Shittu ya kai kara ne a kotun gargajiya da ke zamanta a unguwar Mapo da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Liman Lukman Shittu, ya ce “Abin mamakin shi ne mutumin da ya mayar da Fisayo (matar limamin) sa-dakarsa yana bi na sallah a masallacin da nake limanci?”

Malamin ya zargi matar tasa da kwartanci ne bayan matar ta yi karar shi a gaban kotun tana neman rabuwa da shi.

A masallacina kwartonta ke sallah

A cewarsa, ta hanyar bin mazan da take yi ne ta haifi ’ya’ya uku da suke rikici a kansu.

Tun da farko Shittu ya shaida wa kotun cewa bayan matar tasa ta kwashe kayanta daga gidansa a 2021 ta fara tuka wata dalleliyar mota.

“Fisayo ta rika burga a gari cewa wani dan uwanta ne ya ba ta motar, amma a bincikena na gano cewa kwartonta da suka dade tare ne ya saya mata motar.

“Ya Mai Girma, Fisayo ta fara rawar kai ne tun wani lokaci da na kasa ba ta kudin kama hayar shago.

“Daga lokacin ta daina dawowa gida da wuri, har sai da na yi mata kashedi cewa idan ta kara, to zan kulle gida in bar ta a waje, amma maimakon ta daina, sai kawai ta kwashe kayanta ta bar gidan tare da yaran su uku.

“Ta sauya wa karamin makaranta ba tare da na sani ba, sauran biyun kuma suka ce su ba za su kara dauka ta a matsayin mahaifinsu ba.

“A watan Ramadan da ya gabata na bukaci na tsakiyan ya dawo wurina da zama, amma ya ki; Shi kuma babban, da aka ba su hutu a makaranta, kin zuwa wurina ya yi.

“Abin mamaki shi ne mutumin da ya mayar da Fisayo sa-dakarsa mamu ne a masallacin da nake limanci!”

Mutumin banza ne

Da take nata jawabin, matar mai suna Fisayo, ta ce mijin nata ba shi da dattaku, kuma “Shittu ya yaudare ni na karbo rance daga wani karamin banki bisa alkawarin ni ce zan yi amfani da kudin in fara sana’a, amma ya ki biya.

“A yunkurinsa na cimma manufarsa, har barazanar caka min wuka ya yi min, idan ban tattara kayana na bar mishi gidansa ba. Ga shi kuma mutum ne mai yawan kawo matan banza gidan aurenmu.

“Ya rusa shagon da na gina da kudina na sa kaya a ciki, duk a yunkurinsa na hana ni yin sana’a.

“Yana yawan zagi na, har yakan nesanta kansa da alhakin daukar nauyina da na yaran.

“Duk da cewa ’yan uwansa daga dangin uwa da na uba sun sa baki, dole na kwashe kayana domin in tsira da rayuwata,” a cewar Fisayo.

A je a yi gwajin DNA —Kotu

Bayan sauraron bayanan kowane bangare, shugabar kotun, S. M. Akintayo, ya umarci ma’auratan da su je asibiti a yi musu gwajin kwayar halitta ta DNA tare da ’ya’yan nasu domin tantance asalin mahaifin yaran.

Shugaban kotun ta ce: “Shittu da Fisayo ne za su dauki nauyin gwajin na DNA, kuma za a kawo sakamakon gwajin kai-tsaye ba tare da an bude ba zuwa ofishin rajistaran kotun.”

Daga nan ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Mayu domin a kawo sakamakon gwajin na DNA.