✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Man United ta sha kashi a gidan Leicester, Salah ya kamo Drogba

Kwallaye hudu rigis Leicester City ta jefa a ragar United.

Manchester United ta debi kashinta a hannu yayin da Leicester City ta yi birgimar hankaka da ita a wasan mako na takwas na gasar Firimiyar Ingila ta bana da suka fafata da yammacin ranar Asabar.

Leicester City ta doke United da ci 4-2 yayin karawar ta gudana a filin wasa na King Power da ke birnin Madrid mai daukar fiye da ‘yan kwallo dubu 32.

Wannan wasa dai ana iya cewa reshe ne ya juye da mujiya kasancewar United ce ta fara jefa kwallon farko a wasan ta hannun Mason Greenwood tun a minti na 19 da fara wasa.

Daga nan ne Leicester ta yi azamar farkewa ta hannun dan wasanta na kasar Belgium, Youri Tielemans a minti na 31.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne dan wasan bayan Leicester, Çağlar Söyüncü ya jefa kwallo a ragar United bayan ya samu taimako abokin aikinsa, Ayoze Pérez.

A minti na 82 ne kuma United ta sake farkewa, inda ta jefa kwallonta ta biyu ta hannun Marcus Rashford, ashe rashin sani mai ’ya’ya ya ciwo domin kuwa hakan ya fusata Leicester.

Babu wata-wata Leicester ta jefa kwallo ta uku ta hannun tauraronta, Jamie Vardy a minti na 83, inda kuma ana gab da tashi dan wasanta na kasar Zambia, Patson Daka ya jefa mata kwallo ta hudu.

Da sakamakon wannan wasa dai, United ta koma mataki na biyar a a teburin Firimiyar Ingila da maki 14, wanda za ta iya sauka daga wannan mataki kasancewar akwai wasu kungiyoyin da ba su buga wasanninsu ba.

Ita kuwa Leicester City ta tuke a mataki na 11 a teburin Firimiyar Ingila da maki 11, wanda hakan ya nuna ba ta fuffukar da ta rika yi ’yan shekarun baya bayan haurowarta daga rukunin ’yan dagaji wato Championship.

Salah ya yi kankankan da Drogba

Dan wasan gaba na Kungiyar Liverpool na kasar Masar, Mohamed Salah, ya yi kafada da Didier Drogba a matsayin yan wasan Afirka da suka ci kwallaye 104 a gasar Firimiyar Ingila.

Salah ne ya ci kwallo ta hudu da ta kayatar a wasan da Liverpool ta lallasa Watford a ranar Asabar.

Kwallaye uku Roberto Firmino ya ci a wasan da Liverpool ta lallasa Watford, wasan da aka tashi 5-0.

Sadio Mane ya zama dan wasan Afirka na uku da ya ci kwallo 100 a Premier inda ya fara zura kwallo kafin Roberto Firmino ya ci Watford.

Firmino ne ya rufe da kwallo ta biyar ana dab da tashi daga wasan, karon farko da ya ci kwallo uku rigis tun watan Disamban 2018