✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manchester City ta dauki Erling Haaland daga Dortmund

Erling Haaland zai dinga daukar albashi Yuro miliyan £375,000 a duk sati.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta kammala sayen dan wasan gaban Borrusia Dortmund, Erling Haaland.

Haaland ya kammala kashin farko na gwajin lafiyarsa a kasar Belgium a hannun likitocin Manchester City da ta aike don duba shi.

Yanzu abin da ya rage shi ne dan wasan ya rattaba hannu a kan takardun yarjejeniyar da Manchester City ta shirya tun sati uku da ya wuce.

Manchester City ta shaida wa Borrusia Dortmund cewar za ta biya kudin sakin dan wasan Yuro Miliyan 75 a satin da za a shiga.

Duka kungiyoyin biyu za su sanar da kammala cinikayyar dan wasan a sati mai zuwa da zarar Manchester City ta kammala biyan kudin sakin dan wasan.

Haaland da iyalansa na son a kammala komai cikin wannan satin, wanda hakan zai ba shi damar yin bankwana da magoya bayan Borussia Dortmund.

Erling Haaland ya amince zai dinga karbar albashi daya da dan wasa Kevin De Bruyne, Yuro miliyan £375,000 a duk mako.

Haaland zai rattaba hannun zama a Manchester City na tsawon shekara biyar, wato zuwa karshen kakar wasanni ta 2027.