Manchester City ta kammala cinikin Jack Grealish | Aminiya

Manchester City ta kammala cinikin Jack Grealish

Jack Grealish
Jack Grealish

Manchester City ta kammala daukar Jack Grealish daga Aston Villa kan fam miliyan 100.

An yi hanzarin kammala cinikin domin dan kwallon na Ingila ya samu damar buga wa City wasan Community Shield da za ta fafata da Leicester City a ranar Asabar.

A yanzu Grealish mai shekara 25, ya zama dan kwallo mafi tsada da aka saya a Birtaniya.

Farashin da City ta biya kan Greelish ya zarce fam miliyan 89 da Manchester United ta biya don sake sayo dan wasan Faransa Paul Pogba daga Juventus a shekarar 2016.

A watan Satumban shekarar bara Grealish ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar shekaru biyar tare da Aston Villa.

Kocin City Pep Guardiola ya bayyana kwarin gwiwar cewa kwarewar Grealish za ta karawa tawagarsa karfin maciya kwallo da ake ganin kungiyarsa ta mallaka.