✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manchester City ta lallasa Manchester United

Hakan zai zafafa kiran da magoya bayan Kungiyar suke yi kan a kori Solksjaer.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta doke takwararta, Manchester United, a wasan Manchester Derby da ci biyu da nema.

Dan wasa E. Bailly ne ya ci gida a minti na bakwai, sannan Bernardo Silva ya kara a minti na 45.

A karshen lokaci, Manchester City ta fi taka leda da kashi 67 cikin 100, yayin da ita kuma Manchester United take da kashi 32.

Bugu da kari, Manchester City ta kai hari har sau bakwai, inda a ciki guda biyar suka je kai tsaye zuwa raga.

Ita kuma Manchester United ta kai hari guda uku ne kawai, inda a ciki guda daya ne kacal ya je kai tsaye zuwa raga.

Wannan rashin nasarar da kingiyar Manchester United ta yi, zai kara zafafa kiran da magoya bayanta suke yi kan a kori mai horar da ’yan wasanta, Solksjaer.