✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manchester City ta zama zakarar Firimiyar Ingila

City ta lashe Firimiyar Ingila yayin da ya rage wasanni uku a karkare gasar.

Manchester City ta lashe Firimiyar Ingila ta bana yayin da ya rage wasanni uku a karkare gasar.

Nasarar da City ta samu ta nuna cewa ta lashe gasar karo na uku kenan cikin shekara hudu.

Hakan na zuwa ne bayan da abokiyar hamayyarta, Manchester United ta yi bari a wasan da Leicester City ta lallasa ta ci 2-1 a Old Trafford.

A ranar Asabar da ta gabata ce City ta sa ran lashe gasar yayin haduwar ta da Chelsea wacce ta yi doke ta ci 2-1 a Etihad.

Bayan wasan ne City ta sake zuba idanu don ganin Manchseter United ta sha kashi yayin haduwarta da Aston Villa, inda United ta yi nasara a wasan da ci 3-1.

Sai dai a yanzu Leicester ta tabbatar wa da City nasarar lashe gasar Firimiyar Ingila bayan dukan da ta yi wa United har gida da ke mataki na biyu a gasar da maki 71.