✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manchester United ta sallami kocinta, Ole Solskjaer

Matakin na zuwa ne bayan jerin shan kashin da kungiyar ta yi a kusan wasanni bakwai.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, a ranar Lahadi ta tabbatar da sallamar mai horar da ‘yan wasanta, Ole Gunnar Solskjaer daga mukaminsa.

Korar kocin na zuwa ne bayan jerin shan kashin da kungiyar ta yi a kusan wasanni bakwai da ta fafata a baya bayan nan.

Sanarwar korar na kunshe ne a cikin wani sako da kungiyar ta wallafa a shafinta na Twitter.

“Ole zai ci gaba da zama wani zakaran gwajin dafi a Manchester United, amma cikin alhini muke sanar da daukar wannan mataki mai cike da takaici,” inji kungiyar.

Hukumar gudanarwar kungiyar dai ta gudanar da taro ne ranar Asabar bayan rashin nasarar da ta yi da ci 4-1 a hannun Watford, daya daga cikin rashin nasara mafi muni a tarihin zamansa a kungiyar, inda suka amince cewa hakan ba abin lamunta ba ne.

Rahotanni dai sun ce ko gabanin daukar wannan matakin, dan wasan na da masaniyar abin da zai iya aukuwa da shi, musamman la’akari da yadda magoya bayan kungiyar ke ci gaba da matsin lambar a kore shi.

Solskjaer dai ya fara aiki da kungiyar ne a matsayin koci a watan Disambar 2018.