✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manhajojin Google da ke satar bayananku

NCC ta bankado manhajojin Google da ke satar bayanan mutane

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ja hankalin ’yan kasar kan wasu manhajojin Google Chrome da ke satar bayan mutane.

NCC ta ce akwai wasu manhajojin Google Chrome Extension guda biyar da ke bibiyar abubuwan da mutane suka yi a intanet tare da satar bayanai daga na’urorin da suke amfani da su.

Gargadin da hukumar ta fitar ya ce manhajojin leken asirin su ne: Netflix Party da Netflix Party 2 da FlipShope Price Tracker Extension.

Sauran su ne AutoBuy Flash Sales da kuma Full Page Screenshot Capture Screenshotting.

Hukumar ta ce sama da mutum miliyan 1.4 suna amfani da wadannan manhajojin don haka take kira ga mutane da su yi hattara wajen amfani da Google Chrome Extensions.

“Masu amfani da wadannan manhajojin ba su san cewa suna yi musu kutse da kuma satar bayanai ba.

“Suna bibiyar hadahadar kudade da mutum ya yi ta intanet, sannan suna samun kudaden shiga daga masu shaguna na intanet,” ba tare da sanin mutane ba,” in ji sanarwar.

Ta ce mafi shi ne masu amfani da wadannan manhajojin su goge su, sannan mutane su rika lura tare da tabbatar da sahihancin duk wani sako da ke neman izinin shiga wani shafin intanet kafin fara amfani da shi.

Google Chrome extensions manhajoji ne da ake iya karawa a kan manhajar shiga intanet ta Google Chrome domin inganta yanayin aikinsa.

Ana kuma amfani da su dakile wasu tallace-tallace ko sarrafa kalmar sirri da sauransu.