✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maniyatan Najeriya 2,500 ba za su samu zuwa Hajji ba

Maniyyatan aikin Hajji daga Najeriya kimanin 2,500 na fuskantar barazanar kasa sauke farali a aikin Hajjin bana.

Maniyyatan aikin Hajji daga Najeriya kimanin 2,500 na fuskantar barazanar kasa sauke farali a aikin Hajjin bana.

Kungiyar Masu Jigilar Aikin Hajji da Umrah ta Najeriya (AHUON) ta bayyana cewa sama da maniyyata n su 2,500 da za su bi jiragen yawo 51 za su iya rasa aikin Hajjin 2022, saboda jinkirin  biyan su kudin guzuri.

Rahotanni na nuna kamfanonin sun tura kudin ta asusun ajiya na bai-daya na Hukumar Aikin Hajjin ta Kasa (NAHCON) da ke Babban Bankin Najeriya (CBN) domin tura wa kamfanonin kula da alhazai a da ke Saudiya.

Ana ba wa maniyyata kudin guzuri ne domin biyan kudin masauki da abinci da kuma na zirga-zirga, da kuma biyan kudin biza.

Aminiya da ta gano cewa matukar ba a turawa masu jiragen yawon kudaden ba, babu yadda za su iya kammala tsare-tsarensu da kamfanonin kula da alhazai a Saudiyan.

Kimanin maniyata 42 ne da suka bi jiragen yawo daga Kano dai suka isa Kasa Mai Tsarkin a ranar Talata ba tare da tabbatar musu da Bizar su ba.

To sai dai da saukarsu a kasar, aka jibge su a filin jirgin Muhammad Bn AbdulAziz da ke Madina aka dakatar da su har tsawon kwan guda, kafin daga bisani hukumar NAHCON ta shiga tsakani.

Manajan kamfanin jirgin yawon, Malam Kabiru Sani Babanyaya ya ce kamfaninsa ya yi duk mai yiwuwa ne ya tura maniyatan da suka bi ta hannunsu ne, saboda da sun rasa jirgin Saudi Airline da ya tashi ranar Talata, to za su tafka asarar Naira milyan 50.

Ya ce “Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta agaza mana. Mutane 42 ne lamarin ya shafa, kuma sun samu biza, sauran takwas kuma sai ranar Alhamis za su tashi.”

A nasa bangaren sakataren kungiyar ta AHOUNA, Alhaji Nasiru Chamo, ya shaida wa wakilinmu cewa jiragen yawo 51 ne da maniyata 50 kudin guzirisu bai shiga asusu ba har yanzu a Kasa Mai Tsarkin.