✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maniyyata Kiristoci 300 daga Najeriya sun isa Jordan ziyarar ibada

Gwamnan Jihar Enugu ne ya dauki nauyin maniyyatan

Akalla maniyyata Kiristoci 300 daga Najeriya ne suka isa Amman, babban birnin kasar Jordan domin aikin ziyarar ibada na bana.

Maniyyatan sun isa Amman ne da sanyin safiyar Asabar domin yin aikin ibadar, kuma za su shafe tsawon kwana tara suna yi a wuraren tarihi, kamar yadda suka zo a littafin Baibul.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaio cewa Gwamnan Jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi ne ya dauki nauyin maniyyatan.

A ranar farko ta ziyarar dai, an kewaya da su zuwa wajen tarihi na Citadel, wanda ke kan wani tsauni a kusa da birnin na Amman.

Citadel dai shi ne wajen da mutanen da suka fara zama a babban birnin kasar suka zauna.

A yayin ziyarar dai, maniyyatan sun kuma ziyarci tsaunin Hercules wanda Romawa suka gina, da kuma wani gini da ya zama wani bangare na tsohuwar Daular Umayyad, wacce ta yi tashe a karni na shida, kuma yake dauke da cocin Byzantine.

Kazalika, an ba maniyyatan damar shiga gidan adana kayan tarihi na Jordan domin ganin wasu dadaddun kayan tarihi da hotuna.

Kafin barinsu Najeriya daga Jihar ta Enugu dai, sai da Gwamna Ifeanyi ya hore su da su zama jakadun kasar na gari a can, sannan kada su ksukura su gudu daga wajen ibadar zuwa cikin kasar. (NAN)