✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Maniyyatan aikin Hajjin 2020 za su samu fifiko a 2021

Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jihar Neja ta ce maniyyatan aikin Hajjin 2020 da ba su karbi kudadensu daga wurinta ba za su…

Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jihar Neja ta ce maniyyatan aikin Hajjin 2020 da ba su karbi kudadensu daga wurinta ba za su sami fifiko lokacin tafiya aikin Hajji mai zuwa.

Babban Sakataren Hukumar, Umar Makun Lapai shine ya sanar da hakan yayin da ya  karbi bakuncin Darakta Janar na Hukumar Kula da Harkokin Addini ta jihar, Umar Faruk a ofishinsa.

Ya kuma yi karin haske kan shirye-shiryen da hukumarsa ke yi don ganin ta yi nasara a aikin Hajjin badi.

Ya ce abin da ya rage shi ne matsalar da taso kan sabon tsarin adashin gatan maniyyata aikin Hajji, wanda hukumomin kula da alhazai na jihohi ke tattaunawa a kai.

Ya ce shirin da Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ke kokarin bullowa da shi na neman kawo musu tarnaki.

A cewarsa, duk da yake ba sa adawa da tsarin, zai fi kyau hukumar ta kyale jihohi su yi wa kansu jagora.

Shi kuwa a nasa jawabin, Babban Daraktan Hukumar Al’amuran Addini ta jihar, Alhaji Umar Farouk taya babban sakataren hukumar murna ya yi kan sake nadinsa a shugabancin hukumar tare da yabawa salon shugabancinsa.

Ya ce kiran da ake yi kan a kyale jihohi su kula asusun jin dadin alhazai a jihohinsu mataki ne da ya dace, inda ya yi alkawarin taso da batun yayin taron shekara-shekara na Majalisar Limamai domin a tattauna.