✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Maniyyatan Kano sun yi zanga-zangar rashin samun tafiya Saudiyya

Mun samu labari ma cewa babu kujeru a kasa.

Wasu maniyyatan Aikin Hajji a Jihar Kano sun gudanar da zanga-zanga kan rashin samun tabbacin tafiyarsu kasa mai tsarki wajen sauke farali.

Kimanin maniyyata 284 ne wadanda suka biya kudinsu ta tsarin nan na adashin gata ga Bankin Jaiz ne ba su samu tafiya ba a bana.

Hukumar Alhazai ta Kasa tare da hadin gwiwar Bankin Jaiz ne suka kaddamar da shirin adashin gata mai dogon zango domin saukakawa masu son tafiya Aikin Hajji ta yadda za su rika tara kudin a hankali.

An yaudare mu —’yan adashin gata

Wakilin maniyyatan da suka biya kudinsu ta tsari adashin gata, Alhaji Hassan Zakari, ya shaida wa manema labarai cewa sun dauki tsawon shekaru tun 2019 suna ajiye kudinsu da niyyar tafiya aikin Hajji amma har zuwa wannan lokaci da ya rage kwanaki kadan a fara gudanar da ibadar Aikin Hajji babu sahihiyar magana game da tafiyarsu.

“Jiya [Litinin] rukunin farko na maniyyatan Kano sun tashi amma mu har yanzu babu wata tsayayyarmagana.

“Ba a ba mu jaka ba ballantana unifom. Ba a yi mana allura ba, ballantana a sanya mana ranar tashi.

“Mun samu labari ma cewa babu kujeru a kasa. Wannan shi ne dalilin da ya sa hankalinmu ya tashi.”

Alhaji Zakari ya kara da cewa tuni Bankin Jaiz ya cire Naira miliyan biyu da dubu dari biyar wanda aka rarraba shi a tsakanin Hukumar Alhazai ta kasa da kuma ta Jihar Kano.

Aminiya ta ruwaito cewa maniyyatan sun zargi Hukumar Alhazan Jihar Kano da yaudararsu.

“Hukumar Alhazai ta jiha ta yaudare mu saboda a koyaushe tana nuna mana cewar za mu samu tafiya.

“Domin har ta kai matakin da suka karbi fasfo dinmu domin yi mana biza. Hakan ya sa muka sa rai akan tafiyar. Sai kuma yanzu ga shi mun zama babu tsuntsu babu tarko,” a cewar Alhaji Zakari.

Ba mu da kujerun ’yan adashin gata

Da yake mayar da martani, Babban Sakataren Hukumar Alhazan Kano, Alhaji Abba Dambatta ya bayyana cewa kujerun da Hukumar Alhazai ta Kasa ta ba Jihar Kano guda 2229, kuma babu wani tanadin kujeru da aka yi wa maniyyatan adashin gata na Bankin Jaiz.

“Kun san a bana Najeriya ta samu karancin kujerun Hajji wanda kai tsaye ya shafi Jihar Kano domin a baya ana ba mu kujeru sama da dubu biyar amma a yanzu kujeru dubu biyu aka ba mu.

“Kuma a cikin kujerun nan babu na ’yan adashin gata na Bankin Jaiz a ciki.”

Dambatta ya roki maniyyatan da su kara hakuri domin hukumar tana iyakar kokarinta wajen ganin ta samo musu kujeru daga Hukumar Alhazai ta Kasa.

“A yanzu haka ina kan hanyata ta Abuja insha Allah za mu samu muku kujeru domin ku samu tafiya,” a cewar Alhaji Dambatta.

A Litinin da ta gabata ce rukunin farko na maniyyatan Kano 400 da suka fito daga Kananan Hukumomin jihar guda shida da suka hada da Rano da Kibiya da Bunkure da Dawakin Kudu da Kura da Ajingi suka tafi kasa mai tsarki.