✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maniyyatan Taraba sun nuna damuwa kan hana Aikin Hajjin bana

Hana aikin Hajji na bana na da wata manufa ta daban ba wai don cutar ba.

Maniyyatan da suka biya kudin aikin Hajji a Jihar Taraba sun nuna damuwa kan matakin hana zuwa aikin Hajji na bana da hukumomin kasar Saudiyya suka yi.

Wasu daga cikin wadanda suka biya kudin aikin Hajjin sun bayyana cewa labarin hana zuwa aikin Hajji ya bata masu rai.

Daya daga cikin maniyyatan mai suna Ibrahim Lawal, ya ce hana zuwa aikin Hajji da hukumomin kasar Saudiyya suka yi ya bata wa al’ummar Musulman duniya rai kuma matakin ya saba wa addinin musulunci domin aikin Hajji daya ne daga cikin rukunan musulunci.

Ya ce a shekarar da ta gabata an hana zuwa aikin Hajji saboda cutar Coronavirus sai kuma gashi a wannan shekarar an sake hanawa duk dai saboda wannan cutar.

A cewarsa, ga dukkan alamu yaduwar cutar Coronavirus ya ragu a fadin duniya wanda hana zuwa aikin Hajji na da wata manufa ta daban ba wai don cutar ba.

Ya kara da cewa, mafi yawan wadanda suka biya kudin aikin Hajji a Jihar Taraba an yi masu rigakafin cutar amma sai gashi an hana zuwa aikin Hajji na bana.

Aminiya ta ruwaito cewa, Hukumomi a Saudiyya sun ce jimillar mutum 60,000 ne kacal aka yarda su gudanar da aikin Hajji na bana, wadanda suka kunshi ’yan asali da baki mazauna kasar.